Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Kano Pillars ta yi wasa 13 ba tare da an ci ta ba

Kano Pillars ta yi wasa 13 ba tare da an ci ta ba

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta doke Adamawa United da ci 2-0 a wasan mako na 18. Hakan ya sa Pillars ta yi wasa 13 a jere ba tare da an doke ta ba a gasar cin Kofin Firimiya ta Najeriya ta bana.

Rabon da a doke Pillars tun ranar 20 ga watan Nuwamba, inda Jigawa Golden Stars ta yi nasara a kanta da ci 1-0. Pillars wadda ta buga wasa 16 tana ta takwas a teburi da maki 24, inda ta ci karawa biyar da canjaras tara da rashin nasara biyu.

Kamar yadda kafar labarai ta BBC Hausa ta ruwait. Kawo yanzu Kano Pillars ta ci kwallo 18 inda aka zura mata guda tara a raga. Kwantan wasannin da kungiyar ta Kano ke da su su ne da Enugu Rangers da kuma Enyimba, wadanda suke buga gasar Zakarun Afirka ta Confederation.