✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano ta gudanar da taron tattaunawa na farko a kan wasanni

Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ta gudanar da taron tattaunawa na farko a kan harkar wasanni da nufin lalubo hanyoyin da za a ciyar da…

Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ta gudanar da taron tattaunawa na farko a kan harkar wasanni da nufin lalubo hanyoyin da za a ciyar da harkar gaba.

Taron na yini biyu wanda aka yi wa take da “Harkokin Wasanni a Jihar Kano Jiya da Yau da kuma Gobe: Kyakkyawan Shugabanci, Nasarorin Wasanni da kuma Matsawa Zuwa Gaba,” ya samu halartar manyan masu ruwa-da-tsaki a harkar wasanni daga ciki da wajen jihar.

Tun farko a jawabin maraba, Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima ya ce lokaci ya yi da ya kamata Jihar Kano ta matsa daga matsayin da take kai a harkar wasanni don haka suka gayyato masu ruwa-da-tsaki.

“Mun fahimci cewa ba mu kadai muke da basirar gudanar da harkar nan ba, hakan ya sa muka gayyato masana daga waje don a zauna a tattauna tare da samun shawarwari kan yadda za a ciyar da harkar wasanni gaba. Mun gayyato masana daga jami’a da tsofaffin ma’aikatan hukumar wasanni da jami’an wasanni da masu hannu da shuni da suke daukar nauyin wasanni daban-daban a jihar nan,” inji shi.

Alhaji Galadima ya ce a karshen taron za a  samar da wasu shawarwari ko manhajar da za a mika wa gwamnati wajen gudnar da harkar wasanni a nan gaba.

Da yake jawabi a wajen taron Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje wanda Mataimakinsa Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ya nanata goyon bayan gwamnatin jihar a kan harkokin wasanni.

Dokta Gawuna ya yi kira ga Hukumar Wasannin da ta rika ajiye kwarya a gurbinta, a duk lokacin da aka tashi zabar ’yan wasa.

Ya bayyana cewa da zarar an kammala harkokin zabe Gwamnatin Jihar Kano za ta gudanar da gasar Kofin Ramat wanda aka bayar da sanarwar dage shi a kwanakin baya.

A makalar da ya gabatar, Farfesa Rabi’u Ahmed na Jami’ar Bayero da ke Kano, takardarsa ta mayar da hankali ne kan rawar da Jihar Kano ta taka a wasanni daban-daban a baya. Ya ce tun a 1954  Jihar Kano take fitar da fitattun ’yan wasa wadanda suka yi fice a hakar wasanni daban-daban ba ma kawai a gida Najeriya ba har da kasashen waje.