✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano ta karrama Pillars da ’yan kwallonta na Eaglets

Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar Kano ya karrama ’yan kwallon kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 da ake wa lakabi da Golden…

Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar Kano ya karrama ’yan kwallon kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 da ake wa lakabi da Golden Eaglets da suka fito daga Jihar watau kyaftin din kungiyar Musa Muhammad da kuma Bello Zaharadine inda ya ba kowannensu gidaje da aka kiyasta kudinsu a kan Naira miliyan 15 kowannensu masu daukuna uku a unguwanni da suka zaba watau Unguwar Amana ko ta Bandirawo ko kuma ta Kwankwasiyya.
Haka kuma Gwamnan ya bayar da sanarwar tallafa wa ’yan kwallon da suka fito daga Jihar da kocinsu da kuma jami’an hukumar kwallon kafa ta kasa NFF wadanda suka taimaka  aka lashe kofin duniya na matasa a kwanakin baya da kudi Naira miliyan 9 da dubu 800.
Kazalika Gwamna Kwankwaso ya bayar da sanarwar ba kowane dan kwallon kulob din Kano Pillar da jami’ansu su kimanin 25 mota kirar Toyota Corolla da aka kiyasta kudinta akan Naira miliyan 4 kowacce saboda lashe gasar Premier ta kasa sau biyu a jere.
Gwamnan ya karrama ’yan kwallon ne tare da kulob din Kano Pillars da kulob din kwallon kwando watau Kano Pillars Basketball Team wadanda suka lashe kofin kwallon kwando na Dstb Championsship  na shekarar 2013 a gidan gwamnatin jihar a ranar Talatar da ta wuce.
Kwamishinan yada labarai, matasa da wasanni da kuma al’adu Farfesa Umar Patrick Jibril ya ce gwamnatin jihar ta yi haka ne don saka wa ’yan wasan musamman wajen daukaka martabar Jihar da kasa baki daya wajen lashe kofunan.
Ya ce gwmanatin ta yanke shawarar karrama ’yan kwallon Eaglets ne ganin cewa kyaftin din kungiyar Musa Muhammad da kuma mai tsaron baya Bello Zaharaddin sun fito daga Jihar ce.