Da Dumi Dumi

Kano za ta gudanar da bikin karrama ’yan wasan Arewa

Alhaji Ibrahim Galadima

Za a gudanar da bikin karrama masu harkar wasanni na  Arewa na Prestigious Awards  kashi na biyu a Jihar Kano.

Shugabannin kungiyar da ke shirya bikin sun bayyana haka ne a lokacin da suka kai ziyara ga Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima.

Shugaban ayarin Yusha’u Hamza Kafinchiri  wanda ya wakilci Hajiya Sa’a Ibrahim Magashi ya ce  shugabannin kungiyar sun yanke shawarar mika wa Jihar Kano ragamar gudanar da bikin karo na biyu  ne lura da irin gudunmwar da jihar ke bayarwa a harkar wasanni. “A shekarar 2018 mun gudanar da taron farko a wannan Jiha ta Kano wanda kuma ya kayatar  saboda haka muka ga dacewar mu sake gudanar da bikin a wannan karon ma a Jihar Kano wacce ta mayar da jihohin  Arewa  abin alfahari a harkar wasanni.”

A jawabin Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Ibrahim Galadima ya yaba wa kungiyar bisa ayyukan da take gudanarwa musamman shirya bikin karrama ’yan Arewa wadanda suka bayar da gudunmawa a harkar wasanni.

Alhaji Galadima ya tabattar wa ayarin samun goyon bayan gwamnatin Jihar Kano inda ya yi alkawarin cewa hukumar za ta ci gaba da bayar da gudunmawa ga duk wani abu da zai ciyar da harkar wasanni gaba a Arewacin kasar nan.

ADVERTISEMENT

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya