✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kansila ya tallafa wa mata da matasa a Legas

Kansila Sulaiman Jubril Kiyana daya daga cikin zababbun kansiloli uku ’yan Arewa ke a Jihar Legas, ya dukufa wajen kirkiro tsare-tsaren bai wa mata da…

Kansila Sulaiman Jubril Kiyana daya daga cikin zababbun kansiloli uku ’yan Arewa ke a Jihar Legas, ya dukufa wajen kirkiro tsare-tsaren bai wa mata da matasa tallafi domin kyautata rayuwarsu inda a farkon watan nan ya tallafa wa mata da matasa 100 da suke zaune a barikin soji da na ’yan sanda a Unguwar Obalende a Legas.

Shugaban Karamar Hukumar Ikoyi, Mista Fu’ad Lawal Atanda ne ya jagoranci bikin bai wa mata da matasan barikokin kuma ya yaba wa Kansila Sulaiman Jibrin Kiyana, inda ya ce, Kansilan yana bada tallafin ne a karan kansa ba tare da an ba shi wata kwangila ba ko wasu kudi daga asusun karamar hukumar ba, “Yana bada wannan tallafi ne daga albashinsa, da zan fada maku nawa ne albashinsa, za ku yi mamaki domin ba wasu kudi da suka taka kara suka karya yake dauka ba, amma duk da haka a cikin dan albashinsa ya ware wasu kudi da yake tarawa domin tallafa wa al’ummar da yake wakilta. Wannan abin a yaba masa ne, kuma abin da ya kamata ragowar kansiloli ’yan uwansa su yi koyi da shi. Haka sauran ’yan siyasa masu rike da madafun iko. Kansiloli da shugabannin kananan hukumomi ne suka fi kusa da al’ummarsu, don haka idan suka kyautata mu’amalarsu al’umma za ta kai ga gaci,” inji shi.

Shugaban ya kara da cewa, duk lokacin da Kiyana ya zo masa da maganar shirin da yake yi don tallafa wa al’umma yakan tambayi shi ina zai samo kudin da zai yi, sai ya fada masa akwai ’yan kudin da yake ajiye  su duk lokacin da ya dauki albashi domin irin wannan aiki, wannan shugabanci ne na gaskiya.

Wadansu daga cikin mata da matasan da Kansilan ya tallafawa da jarin Naira dubu biyar -biyar sun nuna farin cikinsu inda suka ce, za su yi amfani da kudin wajen kara jari tare da inganta sana’arsu.

Sulaiman Jubrin Kiyana Kansilan Mazaba ta Daya a Karamar Hukumar Ikoyi/Obalende ya shaida wa Aminiya cewa, duk da yake kudin da ya ba kowane mutum ba wasu kudi ne masu yawa ba, amma yana kyautata zaton za su yi tasiri a rayuwarsu, idan ka lura za ka ga cewa mafi yawansu na yin kananan sana’o’i ne abin da ya hada da sayar da ruwan leda da lemon kwalba da kananzir da makamantan haka, kowanensu idan ya kara Naira dubu biyar a jarinsa za a samu alfanu, “Burina nan gaba in taimaka wa kananan ’yan kasuwa da masu sana’ar acaba a yankin nawa domin za ka ga yawancin masu sana’ar mata ne da matasa wadanda su ne kashin bayan al’umma. Fatata duk wanda ya samu tallafin ya yi amfani da shi yadda ya dace wadanda tallafin bai riske su ba su yi hakuri har a zo kansu,” inji shi.

Ya ce, ya tallafa wa mazauna barikokin soji da na ’yan sandan ne domin jansu a jika kamar  saura jama’ar yanki, sai dai mazauna barikin sun yi korafin cewa, akwai jama’a da dama da aka bai wa tallafin wadanda ba ’yan barikin ba ne duk da cewa, an ware wannan tallafi da nasu ne domin mata da matasan barikin lamarin da kansilan ya ce, zai duba kuma a yi gyara a gaba.