✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanu ya shawarci Ighalo ya ci gaba da yi wa Eagles kwallo

Tsohon dan kwallon kulob din Arsenal da Super Eagles, Nwankwo Kanu a ranar ya shawarci dan kwallon Manchester United Odion Ighalo ya canja shawarar daina…

Tsohon dan kwallon kulob din Arsenal da Super Eagles, Nwankwo Kanu a ranar ya shawarci dan kwallon Manchester United Odion Ighalo ya canja shawarar daina yi wa Eagles kwallo.

Kanu ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da kafar labarai ta Naijanews.com a ranar Litini inda ya shawarci Ighalo da yanzu ke wasa a kulob din Manchester United na Ingila ya canja hukuncin da ya yanke na daina yi wa Eagles kwallo a bara.

Oddion Ighalo dan shekara 30 ya daina yi wa Eagles kwallo ne jim kadan bayan an kammala gasar cin Kofin Afirka a Masar inda Najeriya ta zama ta uku kuma ya zama dan kwallon da ya fi yawan zura kwallo a raga da kwallo 6 a gasar.

Shi dai Ighalo yana wasa ne a kulob din Shenghai Shenhua da ke China amma ya koma Man United  a watan Janairun bana a matsayin aro na tsawon wata shida. Kawo yanzu ya zura kwallo uku a raga a dukkan wasannin da ya yi a United da hakan ya nuna tauraruwarsa na haskakawa.