Categories: Kwalliya

Kara wa kwalliyarki armashi da sarka da dan kunne

Kayan kwalliya na sarka da dan kunne da awarwaro da zobe  suna da matukar muhimmanci ga mace inda kuma yake kara fiddo da kyawun kwalliyar tata.

Idan muka dauki dan kunne za mu ga cewa yana da kashe-kashensa wadanda kuma ake sanya su a lokuta daban-daban.

ADVERTISEMENT

Akwai kanana akwai manya ko mu ce dogaye wadanda kuma ana sanya su ne don su dace da yanayin kwalliyar mace.

Ita ma sarka kamar dan kunne take tana da yanayin kirarta  misali akwai wacce take da kwado akwai wacce take a shimfide.

ADVERTISEMENT

Dukkansu ana sanya su ne daidai da yanayin  kwalliyar mace ko mu ce yanayin yankan wuyan rigar mace. Idan dinkin wuyan zagayayye ne za a sa sarka irinta .

Haka kuma idan wuyan mai fadi ne za a iya sa sarka shimfidaddiya.Sai dai shi zobe da awarwaro ba a cika mayar da hankali wajen zabinsu ba.

Ya danganta da irin wanda mace ke sha’awa ko kuma wanda ya yi daidai da hannunta.

. .

Recent Posts

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano,…

1 day ago