Da Dumi Dumi

Kara wa kwalliyarki armashi da turare

Larabawa na da turare iri-iri da aka fi sani da ‘Arabian Perfumes’ suna daga cikin nau’o’in turare da ake yayi a wannan lokaci.

Nau’o’in turare irin su Rasasi da Ajmal da Oud sun zama nau’o’in turaren da suka fi shahara a cikin turaren Larabawan.

Ire-iren wadannan turare sun samu karbuwa a wajen jama’a da dama saboda yanayin kanshinsu mai sanyaya rai. Har ila yau, irn wadannan turar akwai na maza da na mata daban-daban.

Wani abin armashi da irin wadannan turare shi ne yadda yanayin su yake. Ma’ana yadda zubin turaren yake kasancewa; akwai turaren da yake na mai maiko ne wanda ke da tsinke a ciki inda ake dangwalowa a shafa a jiki, shi irin wannan turare ya fi dadewa a jiki; ma’ana kanshinsa ba ya ficewa cikin sauri. Haka kuma akwai wanda yake na ruwa ne wanda ake fesawa.

ADVERTISEMENT
Share