✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karafunan inji mai sarrafa kansa sun yi shige jikin ma’aikaci

Wani ma’aikaci kamfanin tangaran a kasar China mai suna Mista Zhou mai shekara 49 ya tsallake rijiya da baya, bayan da injin da yake aiki…

Wani ma’aikaci kamfanin tangaran a kasar China mai suna Mista Zhou mai shekara 49 ya tsallake rijiya da baya, bayan da injin da yake aiki da shi mai sarrafa kansa ya yi kuskuren harbo masa wasu karfuna guda goma a jikinsa.

Mista Zhau ya gamu da wannan tsautsayi ne lokacin da yake aiki da injin da daddare a kamfanin kera tukwanen tangaran a lardin Hunan da ke kasar China sai injin ya harbo masa karafunan suka huda jikinsa.

A lokacin da yake aiki da injin ne karafuna masu tsini da tsawo suka cake shi a jikinsa, kamar yadda jaridar The People’s Daily ta ruwaito.

Da farko dai an kai ma’aikacin asibitin unguwar da kamfanin yake, daga bisani aka wuce da shi asibitin Jami’ar Kudu ta Tsakiya a yankin Diangya, saboda munin raunin da ya samu.

Shida daga cikin karafunan sun shiga kafadarsa ta dama da kirjinsa yayin da sauran hudun suka farfasa sauran sassan jikinsa.

Lokacin da likitocin suke yi masa tiyata sun gano cewa, daya daga cikin karafan ya fasa wata jijiyar jini da take taimaka masa wajen kai sako ga kwakwalwa.

Ganin yadda karfunan suka shiga cikin jikin ma’aikacin ya sa ba a yi hoton cikin jikinsa ba, kafin a yi masa tiyata.

“Sakamakon cewa karfunan na da girma don haka ba a da bukatar sanya marar lafiyar a cikin injin hoton binciken ciwo na D-ray, idan kuwa aka saka shi cikin injin, karafunan za su iya sa injin D-ray din ya samu matsala,”  inji Farfesa Wu Pangfeng na fannin tiyata.

An dai yi wa Mista Zhou tiyata inda aka kwashe dare kafn fitar da karafunan. Mista Zhou zai ci gaba da jinya duk da cewa ya fara samun saukin da yake iya motsa hannun damarsa.

Mista Zhou ya samu sa’a rauninsa bai kai na wata ma’aikaciyar wani kamfanin Amurka ba, mai suna Wanda Holbrook wanda injin ma’aikatar ya fille mata kai inda ta rasu.

Wanda mai shekara 57 ta je kusa da injin ne don binciken yadda bangarorinsa  ke aiki, sai kawai wasu karfuna suka fita da daga jiki kamar an harbor mata.

A cewar wani rahoto da kotu ta tattara a shekarar 2015 wani inji ya taba  kashe wani ma’aikacin kamfanin kera kananan motoci a kasar Jamus mai shekara 22.

Mutumin dai yana aiki da kamfanin motocin Baswaja ne inda wani karfe ya cake shi kuma nan take ya rasu.