Search
Subscribe
Karamar Hukumar Jama’a ta gina ofishin ’yan sanda uku

Shugaban Karamar Hukumar Jama’a Danjuma Averik yana miqa wa Eriya Kwamanda na ’Yan sandan Kafanchan mabudan ofishin ‘yan sandan uku

Karamar Hukumar Jama’a ta gina ofishin ’yan sanda uku

Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna ta gina ofishin ’yan sanda guda uku domin bunkasa harkar tsaro, tare da mika su ga babban ofishin ’yan sandan yanki da ke Kafanchan.

Da yake mika mabudan ofisoshin  a bikin da aka gudanar a garin Kogum ranar Asabar da ta gabata, Shugaban Karamar Hukumar Mista Danjuma Peter Aberik ya ce samar da karin ofisoshin ’yan sandan zai taimaka wa harkar samar da tsaro a yankin.

Ya ce an gina tare da wadata ofisoshin da kayayyakin aiki na zamani a garuruwan Kogum d Keyya da Bakin Kogi Kaninkon don bai wa jami’an tsaro saukin gudanar da ayyukansu a yankin.

Shugaban Karamar Hukumar ya yi kira ga jama’ar wadannan wuraren da su bai wa jami’an tsaron goyon baya tare hadin kai wajen taimaka musu da muhimman bayanan da suka kamata don magance miyagun ayyuka a yankin.

Da yake maida jawabi a madadin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Shugaban Ofishin Yanki na ’Yan sanda da ke Kafanchan da ke kula da Kudancin Kaduna, Mista Benshak Dakyer ya mika godiya ga Shugaban Karamar Hukumar da majalisarsa, inda ya bayyana wannan yunkuri a matsayin abin da zai taimaka wa tsaro ta hanyar matso da ’yan sanda kusa da jama’ar kauyuka su samun damar kai dauki cikin gaggawa duk lokacin da aka samu karya doka da oda a yankunan.

Ya yi kira ga jama’ar yankin su bai wa ’yan sandan da za a tura ofishoshin hadin kai da goyon baya don su ji dadin fara gudanar da aiki nan take, sannan ya roki ’ya’yan kungiyar sa-kai ta bijilante a yankin wadanda aka tantance da su hada kai da su don gudanar da ayyukansu cikin sauki.

Jama’a da dama da suka  tofa albarkacin bakinsu sun nuna godiyarsu tare da alkawarin bayar da goyon baya ga jami’an don cimma muradin samar da ofisoshin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin