Da Dumi Dumi

Karamar Hukumar Sanga za ta hada kai da takwarorinta na Nasarawa don dakile ayyukan ta’addanci a iyakokinsu

Karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna ta bayyana shirin da take yi na hada kai da kananan hukumomin Jihar Nasarawa da ke makwabtaka da ita don dakile ayyukan ’yan bindiga da suka addabi yankin.

Shugaban Karamar Hukumar Mista Charles Danladi ya bayyana haka jim kadan bayan zaman da ya gudana tsakaninsa da Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Muhammed Hussain a  Hedkwatar Karamar Hukumar da ke Gwantu, inda suka tattauna yiwuwar samar da hadakar ’yan kungiyar sa-kai don rage hare-hare a yankin.

Da yake yi wa Aminiya karin haske ranar Asabar, Mista Charles Danladi ya nuna damuwarsa kan yadda ayyukan ’yan bindigia ke neman kazanta a yankin, inda ya ce ba za su ci gaba da nade hannuwansu su zura ido batagari na cin karensu ba babbaka ba.

Ya bayyana niyyarsa ta hada kai da duk masu ruwa-da-tsaki da suka hada da kananan hukumomin Jihar Kaduna da shugabannin kungiyar Miyetti Allah na Karamar Hukumar Jama’a da ke makwabtaka da ita da kuma wasu kananan hukumomin Jihar Nasarawa don tabbatar da tsabtace kan iyakokinsu daga marasa son zaman lafiya a yankin.

Haka kuma Karamar Hukumar ta Sanga ta raba wa mutanen kauyen Nandu da rikicin ’yan bindiga ya shafa a farkon shekarar nan kayan agaji da suka hada da kwanon rufi bandir 39 da katakai da kusoshi don  gyara muhallansu da aka kona a lokacin harin da aka kai musu.

ADVERTISEMENT

A lokacin da yake mika kayan tallafin ga wadanda abin ya shafa, Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Abubakar Umar ya nanata wa jama’a bukatar da ke akwai ta yin amfani da kayayyakin wajen gyara muhallansu maimakon karkatar da su ta wata hanya.

Share