✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karar fashewar batura ta haifar da rudani a tashar mota a Abuja

Matafiya da masu gudanar da harkokin kasuwanci da sana’o’i a babbar tashar mota da a ka fi sani da “Jabi Gareji” da ke yankin Utako…

Matafiya da masu gudanar da harkokin kasuwanci da sana’o’i a babbar tashar mota da a ka fi sani da “Jabi Gareji” da ke yankin Utako Abuja, sun shiga halin rudu a ranar Juma’a bayan wani shagon cajin batir da ke wajen ya kama da wuta.

Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 10 na safe, Aminiya ta samu labarin cewa hakan ya sa jama’a da dama gudun da ba su shiryawa ba, kan zaton bama-bamai ne ke tashi, a sakamakon yadda batura da ke cikin shagon, su ka dau tsawon lokaci su na fashewa, daya bayan daya.

Wani jami’in Kungiyar direbobi na tashar mai suna Abdulmalik Ja’afar Danwata, ya shaidawa wakilinmu cewa, ana zargin wutar ta fara ne a sakamakon fesawar wuta (spark), da daya daga cikin tarin batura da ke shagon ya yi.

Ya ce, “Batura sun yi ta kara suna tashi tare da burma rufin shagon, kafin daga bisani jami’an ‘yan kwana kwana da su ka isa wajen da misalin karfe 11 na safe, suka shawo kan lamarin,” in ji shi.

Abdulmalik, ya kara da cewa ba a samu rasa rai ba ko rahoton wani rauni a lamarin, sai dai ya ce an fuskanci asarar dukiya inda wasu suka yi amfani da rudanin da lamarin ya haifar, suka rika sace kayan wasu da ke kasuwanci a wajen da su ka gujewa asarar ransu.

Hakanan ya ce, kamar shaguna biyu zuwa uku da ke makwabtaka da shagon da lamarin ya faru, sun fuskanci ‘yar matsalar wuta da ta fara taba na su rufin shagunan, amma bai kai ga konesu ba, kamar yadda ya yi bayani.

Wani shagon cajin batura ke ci da wuta a yayin da batura ke ta bindiga a garejin motoci na Jabi Gareji, da ke yankin Utako Abuja a ranar Juma’a.