Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Karatun Tsangaya: Yadda almajirai suke gararamba a titunan Abuja

Babban Limamin masallacin Juma’a na Deidei Abuja, Malam Abubakar Ibnu Abibakar
Babban Limamin masallacin Juma’a na Deidei Abuja, Malam Abubakar Ibnu Abibakar

A kwanakin baya ne aka rika cece-ku-ce kan yunkurin da aka ce Bishop din Cocin Katolika na Sakkwato Fada Mathew Hassan Kukah yana yi don ceto rayuwar almajirai da dama. Masu sukar yunkurin nasa suna suka ne kawai, maimakon su waiga su dubi halin da rayuwar almajiran take ciki na tabarbarewar tarbiyya da sauran matsalolin da suke damunsu Aminiya ta zanta da wadansu almajirai da masu ruwa-da-tsaki a kan lamarin da suka hada da malaman Tsangaya da kuma wadaansu shugabannin al’umma, inda gaba dayansu suka amince cewa lamarin na bukatar dauki na gaggawa:

Matsalar tabarbarewar tarbiyya da shiga halin ukuba a tsakanin almajiran makarantun Tsangaya suna kara munana, sakamakon yadda iyaye ke tura yara ciki har da ’yan kanana sosai zuwa makarantun a garuruwa ko birane ba tare da yi musu tanadin rayuwa ba.                                                                                                                                                   Yawancin yaran wadanda iyayensu ke danka su ga hannun malamai ko gardawa ’yan asalin kauyukansu da nufin yin karatu a gabansu a garuruwan da suka tare da su, na bata lokaci mai tsawo a wuraren bara a maimakon kasancewa a tsangayoyinsu, inda suke yawatawa a wuraren tsayuwar motoci kamar tashoshi ko kasuwanni da gidajen sayar da abinci da sauransu.

ADVERTISEMENT

Wadansu almajrai da suke bara a wani wurin tsayawar motoci a kan babban titin Kubwa zuwa Abuja sun shaida wa Aminiya cewa su ’yan asalin yankin Damagari ne a Jihar Kano da suke karatun Tsangaya a garin Deidei a wajen wani malami mai suna Malam Sulaiman, wanda wakilinmu bai kai gano inda yake ba a lokacin da ya ziyarci garin. Almajiran duk da cewa sukan yi fashin karatu ne a ranakun Alhamis da Juma’a kamar yadda suka yi bayani, don su samu damar zuwa wajen don yin bara.

Sun bayyana cewa malaminsu ya yi musu karin ranar Litinin, a lokacin da wakilin namu ya nuna musu cewa, yaya aka yi suka fito yawon bara a garin duk da cewa ba ranar hutu ba ce? Haka nan sun ce suna kai wa malaminsu Naira 50 sannan matar Malam Naira 30 daga cikin kudin da suka samu na sadaka a duk lokacin da suka samu fitowa.

ADVERTISEMENT

“Muna fara karatu ne bayan Sallar Asuba sannan kamar karfe 7:00 (na safe) sai mu tashi mu tafi bara don neman abin karyawa. Bayan nan za mu dawo kamar karfe 9:00 na rana, daga nan sai mu tashi karfe 11:00 na rana sai kuma bayan Sallar Azahar kamar karfe 2:00, sai mu sake komawa wajen karatu,” inji alamjiran.

Sun ce a karshe suna tashi karatu kafin Sallar Magariba sai kuma washegari su sake komawa karatun. Sai dai ganinsu a wajen tsayawar motar tun kafin lokacin Sallar Azahar tare da ci gaba da kasancewa a wajen har zuwa bayan Sallar La’asar ya sanya ayar tambaya a kan ikirarin nasu, na kasancewa a wajen karatu a ire-iren wadannan lokaci.

Wani daga cikin masu karantarwa a wata makarantar Tsangaya a garin Deidei mai suna Malam Adamu Muhammad, wanda ke matsayin Na’ibi ga Babban Malamin Makarantar, Malam Muhammadu Musa, ya ce makarantar tsangayarsu ta shafe sama da shekara 18 da kafuwa. Ya ce su ’yan asalin garin Dawakin Kudu ne da ke Jihar Kano, kuma ya ce yawancin almajiransu sun fito ne daga yankinsu, sai dai a cewarsa akwai daidaikun dalibai daga wasu jihohin Arewa kamar Katsina da Jigawa a makarantar.

Haka ya ce akwai dalibai ’yan je-ka-dawo da ke tare da iyayensu a garin, wadanda aka kebe su a wuri daban kamar kuma yadda suturar da ke jikinsu ta bambanta da na yaran da ke sashin almajirai.

Da yake tsokaci a kan halin da almajiran ke ciki a halin yanzu, malamin ya ce al’amuran karatun Tsangaya sun cakuda kwarai. Ya ce akwai almajirai da ke fita daga tsangayoyi suna yawace-yawaacen bara, sai dai ya ce da yawa daga cikinsu ba hakikanin almajrai ba ne, yara ne kawai da ke yawo haka nan.

“Ban ga dalibanmu a cikin wadanda ka nuna a hoton ba, kuma su ma wadannan da ka nuna da za ka rutsa su a kan su nuna maka makarantar da suka fito, za ka samu da dama daga cikinsu ’yan gari ne kawai ba almajirai ba, kuma ire-irensu na yawon neman abin hannu ne kawai,” inji shi.

Ya ce dalibansu na dogaro da bara don cin abinci sannan suna ayyuka kamar zubar da shara ga jama’a da sauransu don neman kudin da za su sayi sabulun wanki da wanka da sauran bukatu. Malamin ya ce babu wani tallafin kudi da suke samu daga hannun yaran kuma ba wani haraji da suka dora musu a duk lokacin da suka fita yawon neman sadaka. Sai dai ya ce sukan karbi Naira 20 zuwa 30 daga hannun dalibai ’yan gari da ke tare da iyayensu duk ranar Laraba ga wadanda suka samu zarafi. “Ribarmu kawai ita ce muna karantar da su fisabilillahi kamar yadda mu ma malamanmu suka karantar da mu,” inji shi.

Ya ce babu wani tallafi na hukuma daga cikin matakan gwamnati 3 da suka taba samu a tsawon shekara 18 da suka fara wannan aiki, in ban da ’yar sadaka da suke samu daga bayin Allah lokaci-lokaci.

Malam Abubakar Ibnu Abibakar wani Limamin Masallacin Juma’a a garin Deidei da ke Abuja, daya daga cikin garuruwa da ke da almajirai a yankin birnin tarayyar, ya ce ya kamata iyaye masu sha’awar ’ya’yansu su karanta Alkur’ani su rungumi tsarin karantarwar addini cikin sauki da zamani ya kawo a yanzu, wanda zai bai wa ’ya’yansu sanin Kur’anin a cikin Tajwidi tare da sanin sauran bangarorin karatu na addini da makarantun Islamiyya ke samarwa.

Malamin ya ce tsarin almajiranci da a yanzu ke kara gurbacewa sakamakon halin da almajiran ke samun kansu a ciki, ya faro ne lokacin da ake da karancin malaman addini. Ya ce ’ya’ya babbar amana ce a hannun iyaye da Allah zai tambaye su yadda suka kula da su. Saboda haka ya ce ba daidai ba ne iyaye su bar ’ya’yansu suna bara a kan tituna ko tashoshi a yayin da a wani zubin har da gidajen karuwai, inda ya ce hakan ya saba wa tsarin addinin Musulunci.

Aminiya ta zanta da wani kwararre a harkar koyar da yara ilimi mai suna Malam Hudu Danjuma wanda a baya ya rike mukamin Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Suleja, kuma a yanzu shi ne Ko’odinetan Tabbatar da Samar da Ingantaccen Ilimi a Masarautar wadda ta kunshi kananan hukumomin Gurara da Tafa da Suleja, ya ce tsarin makarantar Tsangaya a zamanance ya faro ne a lokacin marigayi Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa amma aka fara aiwatar da shi a karshen mulkin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan inda gwamnatinsa ta kakkafa makarantun. Ya ce a lokacin ne aka bude makarantar Tsangaya ta garin Suleja da wata irinta a Bida da Kwantagora sai kuma a Minna babban birnin Jihar Neja, kuma aka kulla alaka da karin wasu makarantun Tsangaya 5 a Minna; inda suke samun tallafi daga Sarkin Suleja, Malam Auwal Ibrahim, wanda ke matsayin shugaban makarantun a jihar.

Ya ce tsarin makarantar Tsangayar wanda ya hada da koyar da yara ilimin addini da na boko da na sana’a na tsawon shekara 6, zai taimaka idan Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da fadada shi.

A lokacin da Aminiya ta ziyarci makarantar Tsangaya ta Suleja, wadda a yanzu haka ke cikin hutu kasancewar tsarinsu na tafiya ne da hutun makarantun boko, ta gano cewa yawancin dalibai da ke karatu a wajen ba almajirai ba ne, illa yaran marasa galihu da iyayensu ke da zaune garin sai kuma marayu, kuma ana koyar da su ne kyauta a kuma ciyar da su.

Sai dai game da halin da makarantar Tsangaya ta Suleja ke ciki, Malam Hudu Danjuma, ya ce hakan ya faru ne sakamakon kin amincewa da malaman Tsangaya suka yi na su bar almajiransu su rika zuwa makarantar, maimakon karantar da su a tsangayoyinsu na kansu. Ya ce makarantar na da kayyadadden adadin dalibai da za ta iya dauka.

Ya ce ire-iren daliban da makarantar ke koyarwa wato ’ya’yan marasa galihu, su ne dama ke komawa almajirai, saboda haka ya ce makarantar ba ta kauce wa tsarinta ba. Ya ce gwamnatin jihar na taimakawa da kayan abinci da ake ciyar da daliban, haka kuma tana ba da wani kason kudi da ake bai wa malaman da ke koyarwar a matsayin tukuici duk da cewa abin da ake ba sun bai kai na sauran makarantun boko ba, inji shi.

Wani jagoran al’umma a Abuja, Alhaji Hayatuddin Muhammad, ya ce dole Gwamnatin Tarayya tare da gudunmawa daga gwamnatocin jihohi su kawo dauki ga makarantun Tsangaya a matsayin riga-kafi na magance matsalar fitsara da kuma ta’addanci daga tushe. Ya ce yakar matsalar a matakin magancewa kadai inda ake kashe makudan kudi, ba zai iya kai wa ga magance daukacin matsalar almajirai ba.

Yunkurin jin ta bakin hukuma ya ci tura, inda Aminiya ta nemi jin ta bakin Hukumar Ilimi Bai-daya a yankin Birnin Tarayya (UBEB), kan ko akwai wani tanadi na shigo da almajirai a cikin tsarin ta hanyar samar masu da wani tallafi, bai samu nasara ba.

Lokacin da wakilinmu ya je ofishin hukumar a ranakun Talatar da ta  gabata, wani mai taimaka wa Babban Daraktan hukumar, Dokta Adamu Jatau Noma ya shaida masa cewa Daraktan na halartar wani taro da jami’ansa a ofishin. Sannan bayan ya koma washegari Laraba, jami’in ya shaida masa cewa Daraktan yana gudanar da wasu muhimman ayyuka; saboda haka ba zai samu ganinsa ba.