✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karayar kashi: Sabubbanta, matsalolinta da kuma hanyoyin kariya

Tambayar tamu ta yau a kan karaya ce, wadda mai tambayar ke cewa: Wata nawa ake karaya ta doru, watau idan mutum ya karye wata…

Tambayar tamu ta yau a kan karaya ce, wadda mai tambayar ke cewa: Wata nawa ake karaya ta doru, watau idan mutum ya karye wata nawa yake ya warke? Babba wata nawa, yara kuma wata nawa? Da dorin gida da na asibiti wanne ya fi? Na gode.
Daga Amina, Kano.
Amsa: Wannan tambaya ta ki tana da matukar amfani, domin a lokuta da dama akan samu matsalar karaya sosai kuma a yi ta ja-in-jar wanda zai dora mutum, a asibiti ko a gida, domin a mafi yawan lokuta ana gwadawa a ga an samu nasara da dorin gida.
Haka kuma kamar yadda kika kara tambaya, akwai bambancin karayar yara da ta manya. Kafin a gane bambancin, ya kamata da fari mu dan yi shimfida a kan shi kansa kashi. Akwai kasusuwa kusan dari biyu da saba’in (270) a jikin sabon jariri, ana girma wasu na hadewa da juna har a samu dari biyu da shida (206) a babban mutum. Kin ga ke nan yara sun fi manya yawan kasusuwa a jiki. kashin da ya fi girma a jikin dan Adam shi ne kashin cinya, wadanda suka fi kankanta kuma su ne na kunne. Dukkansu sukan iya karewa. Ban da buguwa ta hadari ko faduwa, cututtukan daji da na rashin sinadaran calcium (musamman a tsofaffi da yara), su ma suna kawo karaya.
Akwai karaya iri-iri da ta tsaye (tsagar kashi) da ta kwance, da ta gicciye da wadda ta gutsuttsure. Wasu lokuta bayan karewar har da gocewar kashin ma, wato ya karkace daga saitinsa gaba daya. Wani lokaci kuma a samu karaya fiye da daya a wurare daban-daban a jikin kashi daya. bangarorin jiki da aka fi samun karaya idan an bugu sun hada da kasusuwan hannu da kafa da cinya da kokon kai da kashin kafada da na hakarkari. Mai ciwon daji kuma ya fi samun karaya a kasusuwan gadon baya. Tsofaffi kuma sun fi samun karaya a kashin kugu da na cinya, wani lokaci saboda rashin sinadarai, wani lokaci kuma saboda yawan faduwa.
Alamomin karaya sun hada da jin ciwo mai tsanani da kumburi a wurin da abin ya faru. Akwai kuma kasa yin amfani wurin da ya karye din. A wasu lokuta, fata da naman wurin sukan fashe a ga kashi kuru-kuru.
Karayar manya ta bambanta da ta yara, tun da kashin yaran bai kai kashin manya kwari ba. Ba kasafai ma akan samu kashin yara ya karye ba sai dai ya dan lankwashe ko ya tsage tun da langwai ne. Abin da ya fi kawo karaya a yara shi ne yawan wasan banza kamar hawa bishiya da yawan bugu a gida ko a makaranta (bugu irin wanda bai kamata a yi wa yaro ba), sai kuma ciwon sikila da rashin sinadaran calcium a abinci, wanda wannan tuni mun yi bayanin irin abincin da za a same su. Kuma kashin yara ya fi saurin warkewa idan aka samu karaya tun da kashinsu yana kan girma ne.
Idan mutum ya karye aka kai shi asibiti, da farko za a fara ba shi magungunan kashe zogi, ga na kashe kwayoyin cuta da na barci da dai sauransu, daga bisani a dauki hotunan wurin domin a tabbatar cewa karayar ce kuma wace iri ce. Ta nan ne za a dauki matakin da ya dace. A lokacin ne za a fada wa maras lafiyar ko tiyata ce ta fi, ko kawai daidaita kashin za a yi a wurin a daure.
Wannan duka a gargajiyance ba mu san ko ana haka ba. Duk da cewa ana samun sa’a sosai a mafi yawancin lokuta idan an yi dorin gida, mutane da dama sukan warke da dingishi idan a     kafa karayar take abin da ke nufin kashi maras karayar ya fi mai karayar tsawo, wanda bai kamata a samu haka ba. Banda wannan ma an sha samun dorin gida da aka daure wurin karayar tamau ta yadda jini ya kasa zagawa, daga karshe dai sai yanke wurin ake yi.
Sau da yawa a asibiti akan samu cewa ba sai an yi tiyata ba, kashin da kansa zai hade in dai an daure wurin. Shi ya sa za ki ga wasu an daure kafarsu da jikin gado an daura nauyi an kuma bar shi nan kwana da kwanaki kamar ba abin da ake masa. To a wannan lokacin ne waraka kan samu. Idan aka saki mutum ya motsa wurin, karayar za ta iya gocewa idan lokacin warakarta bai yi ba.
To ko ma dai tiyatar aka yi ko kuma kawai dorin waje aka yi (wato a ja saisaita kashin su hau kan juna), akan daure wurin karayar tsawon kusan wata uku, dangane da yadda karayar ta zo. A wadannan lokuta ana masa allurai iri-iri na kiyaye shi daga kwayoyin cuta da bugun zuciya da sauransu, tun da mutumin da ke kwance wata da watanni yana cikin hadarin kamuwa da wadannan larurori.
Idan kashi ya karye, zai dauki sati shida (6) kafin ya fara daukar hanyar warkewa, daga wannan lokaci zuwa wata uku ne za a iya cewa kashi ya doru, a lokacin ne za a iya motsa kashin ba tare da an ji wani zafi ba, za a iya tafiya ma misali. Amma karaya ba ta warkewa dungurungum sai an samu kimanin shekara daya da rabi. kashin yara yakan dauki rabin wannan lokaci.
Kyakkyawan yanayi na muhalli da abinci mai gina jiki da mai sinadarai irinsu calcium suna taka rawar gani wajen kawo saurin warkewar karaya. Duk wanda ya karye kuma ya rasa wadannan to ba abin mamaki ba ne karayarsa ta dauki fiye da wata uku ba ta hade ba.
Tun da mun fadi abubuwan da kan kawo karaya, hanyoyin kariya daga samun karaya ke nan ba su da wahalar bi kuma sun hada da hanyoyin kariya daga samun hadurran abin hawa, wadanda muka yi bayaninsu a wannan shafi a baya, sai kuma yawan zuwa asibiti duba lafiya (akalla sau daya a shekara), kada mutum ya samu ciwon daji bai sani ba, domin wasu cututtukan dajin ba su da alamu, tunda mun ce ciwon daji zai iya kawo karaya. Sai kuma daina bugun yara don kada su samu karaya da kiyeye su ga barin wasannin banza kamar hawan bishiya. Sai kuma yawan ba su abinci mai gina jiki mai dauke da sinadarin calcium, da su da tsofaffi.

LAFIYAR MATA DA YARA

A yau wannan fili zai amsa
tambayoyin da aka samu

Likita wai da gaske ne a likitance idan wata mace mahaifarta ta lalace (wato da ba zai iya rayuwa a cikinta ba), ana iya daukar kwayayen haihuwa na mijinta da nata a sa wa wata mace daban a mahaifarta, abin da ake kira ‘surrogate mother’? Kuma idan ta haihu wai dan ba nata ba ne na wadannan ma’auratan ne? Idan aka sa mata maniyyin namiji ba haduwa yake da kwayayenta ba? Shin ana uwa uku ne?
Daga Ummu, Gombe
Amsa: Wannan tambaya taki tana da amfani, domin wannan mau’du’i yana da sarkakiya. Akan samu mutane da dama sun yi shekara da shekaru da aure amma ba su samu alherin ’ya’ya ba. Kashi arba’in cikin dari matsalar a maza ne, kashi arba’in a matar, kashi goma matsalar duk su biyun ne, sauran kashi goma ba a san dalili ba.
Abin da na fahimta shi ne, tambaya biyu kika yi a cikin daya. Ta farko ita ce ta ma’aurata wadanda ruwan kwansu yana da kyau duk su biyun, su mahaifa kawai suke nema inda za a dasa dan tayi. Ta biyu kuma kika ce idan aka sa wa wata mata daban wadda ba matarsa ba kwan namiji kawai ba kwan mace.
To kowane bayani na da mazauninsa. A binciken kimiyya, duk wannan na iya faruwa ba matsala. A binciken addini ne ake da shakku. A mazaunin amsa ta farko akan iya sa dan tayi (wato kwan ma’urata namiji da na matar) a mahaifar wata mace daban saboda ta ba shi mazauni da abinci ya girma ya kai wata tara ta haife ta dawo da shi, daidai da yadda aka yarda a kai wa wata mace daban ta shayar da jariri idan uwar ba za ta iya ba, idan ta yaye ta dawo da shi. A mahaifarta mazauni da abinci kawai zai samu, ba kwan cikinta ba. Amma kin ga ba kowane malamin addini ne ma ya yarda cewa a iya samun kwan ma’aurata a sa su ’yar kwalaba ba, idan ya zama dan tayi a mayar mahaifar matar, balle ma a ce a je a sa wa wata mace daban.
Mazauni na biyu shi ne inda matar ba ta da kwayaye, sai a kwashi kwan namiji kadai a sa wa matar da ba a daura musu aure ba, domin ita ta ba da nata kwan. Wannan kin ga kai tsaye ya saba addini. To idan likita ya ba ma’aurata shawara irin wannan, yana da kyau su samu sanannen malamin addini wanda ransu ya kwanta da shi, ya ba su shawarar da ta dace.