Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kare ya shekara daya da rabi a inda mai shi ya yi hadari

Lokacin da karen yake jiran mamallakinsa bayan hadarin mota
Lokacin da karen yake jiran mamallakinsa bayan hadarin mota

Wani kare ya sanya tausayi a zukatan miliyoyin jama’a bayan da aka gano ya yi wata 18 a gefen hanyar da mamallakinsa mai suna Haris ya rasu sanadiyyar hadarin mota.

Karen da ake yi wa lakabi da Greek Hachiko yana kaunar wanda ya mallake shi. Karen jinsin Akita ya yi jiran shekara daya da rabi don ganin mamallakinsa bayan ya mutu a hadarin da ya yi a kusa da wata tashar jirgin kasa a Japan. Rahoto ya ce, farin karen yana ta rayuwa ne sama da shekara daya da rabi a gefen hanyar zuwa birnin Greek a Nafpaktos da ke kasar Girka.

ADVERTISEMENT

Duk da kokarin da wadansu jama’a suka yi don korar karen daga wurin ya ci tura ta yadda idan suka kori karen sai ya sake dawowa wajen da mamallakinsa ya yi hadarin.

Haris mamallakin karen, wanda ya rasu yana da shekara 40 rasuwarsa ta razana jama’a da dama.

ADVERTISEMENT

A ranar 9 ga Nuwamba 2017 wani dan uwan Haris ya rasu a irin wannan hadarin motar da ya yi, kuma a kusa da inda Haris ya yi hadari ya rasu. Duk sun rasu ne a hanyarsu ta komawa gida. Sai dai rasuwar Haris ta bambanta da ta dan uwansa saboda hadarin da Haris ya yi ya fi muni kuma hakan  ne ya sa karensa ya tare a hanyar da hadarin ya faru da nufin ko Haris, zai tashi ya ci gaba da rayuwa, da haka ya zauna a wurin sama da shekara yana jira.

Rahoton bai bayyana ko karen na cikin motar lokacin da hadarin ya faru ko yadda aka yi ya san inda motar ta yi hadari har ya tsaya a wajen da abin ya faru ba. Sai dai jama’ar yankin sun tabbatar da cewa, karen ya zauna a kusa da inda Haris ya yi hadari ya rasu.

Bayan da jama’ar garin suka yi kokarin canja wa karen wajen da yake zaune zuwa wani lokaci sai ya sake dawowa daidai inda Haris ya yi hadarin. Daga nan jama’ar suka fara kawo wa karen abinci da ruwan sha kullum. Bayan karen ya ci abinci sai ya koma ya kwanta ya yi kamar yana jiran Haris, ya taso su tafi gida.

Karen, duk yanayi na zafi ko sanyi bai canja wajen da yake zaune kullum a cikin dajin kusa da wani waje da ake yin bauta.

Tun lokacin da kafar sadarwa ta  Nafpaktia News ta Gikra ta wallafa wannan rahoton tare da bidiyon karen yana jiran Haris, jama’a da dama suka yi ta bayyana ra’ayoyinsu a kafar YouTube.

Irin wannan jinsi kare yakan kasance mai nuna kaunar ga mamallakinsa, musamman idan wani mummunan abu ya same shi, kuma an ce suna iya bayyana alhinin su a fili kamar ba dabba ba. Idan ba a manta ba kwanakin baya an samu rahoton irin wannan jinsin karen a kasar Ajentina, lokacin da ’yan sanda suka tsare mamallakin wani kare a ofishinsu amma karen ya rika kwana a ofishin ’yan sandan har sai da aka saki wanda ya mallake shi kafin ya bar harabar ofishin ’yan sandan.