Daily Trust Aminiya - Kareti: Najeriya ta ci lambobi a Mali
Subscribe

Kareti: Najeriya ta ci lambobi a Mali

Najeriya ta ci lambobin zinare biyu da azurfa tara da tagulla bakwai a gasar Kareti ta kasashen Afirka ta Yamma ta farko da ake gudanarwa a kasar Mali.

Jagoran ayarin Najeriya a gasar kuma Shugaban Kungiyar Wasan Kareti ta Kasa (NKF), Mista Silas Ali Agara ya shaida wa Aminiya cewa, “A ranar farko, Najeriyta ta doke abokan wasa inda ta samu zinare daya da azurfa 5 da tagulla 5 a birnin Bamako na kasar Mali.

Mista Silas Ali Agara ya ce, gasar ta kasu kashi biyu ne, kashi na farko shi ne na masu yin takara daidaiku da kuma na masu karawa a matsayin rukunin ’yan uku.

Shugaban ya ce, “A ajin manya na mata, Elizabeth Oghenebwogaga ta samu azurfa, yayin da Oluwasuen Olurunbe, da Taiwo Fagboro da Kehinde Fagbori suka kai Najeriya ga nasara inda suka ci tagulla, sannan Oluwasuen Olurunbe ya samu tagulla.”

Mista Silas Ali Agara wanda tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawaa ne ya ce a ajin matsakaita, Najeriya ta ci zinare ta hannun Goldfirst Uhoka-Sampson, sai Amarachi Nwankwo ta ci azurfa,. Borishade Emmanuel ita ma ta ci, sannan Basheer Opeyemi ya ci tagulla.

A ajin kanana kuwa, Akuma Onyinye, ta ci tagulla, Akachulwu Ozojideofor ta ci tagulla, sai Christiana Daniel  ita ma ta ci tagulla.

Bugu da kari, a wuni na biyu na gasar, Najeriya ta samu zinare daya da azurfa 4 da tagulla 2. Jimilla tana da zinare 2 da azurfa 9 da tagulla 7.

Kasashen Afirka ta Yamma 15 ne ke karawa a gasar da Najeriya ta  tura ’yan wasa 20 da shugabanni 8.

texem
More Stories