✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin albashi da gwamnati ta yi abin dariya ne – Babban Fadan Kalaba

Shugaban Cocin Darikar Angalika na Kalaba Fada Tunde Adeleye, ya ce karin albashi da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda Shugaban Kasa ya sanya wa hannu…

Shugaban Cocin Darikar Angalika na Kalaba Fada Tunde Adeleye, ya ce karin albashi da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda Shugaban Kasa ya sanya wa hannu ya zama doka abin dariya ne.  Shugaban ya bayyana haka ne a ganawar da ya yi da manema labarai ranar Litinin a harabar cocin da ke Kalaba a Jihar Kuros Ribas.

Babban Fadan Angalikan, ya ce abin dariya ne karin albashi daga Naira dubu 18 zuwa Naira dubu 30, ai gara jiya da yau domin karin albashin bai da wani amfani ga ma’aikaci yanzu. Ya ce “Gwamnatin Tarayya ta yi karin albashi na Naira dubu 30, ga ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni alhali a da can mafi kankantar albashi na Naira dubu 18 yana daidai da Dalar Amurka 111 ne. Karin yanzu da aka yi ya fi muni da lalacewa gara jiya da yau domin Naira dubu 30 da aka mayar da albashin idan aka kwatanta da Dalar Amurka yanzu tana daidai da Dala 83 ne. Shin baya muka ci ko gaba?”

Da yake yin tsokaci game da makomar kasa shugaban cocin ya bukaci a sake fasalin kasar nan lamarin da ya bayyana shi da cewa, “Ana yin kashin dankali.”

Da aka tambaye shi kan matsaloli da ya jero na gazawar gwamnati idan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gayyace shi su gana me zai ce masa?  Sai ya kada baki ya ce, “Sai in ce masa ka yi kokari sannu da kokari Shugaban Kasa amma ka sauka daga mukaminka domin shi ya fi sauki.” Game da ko me ya sa ya yanke shawarar zai fada wa Shugaban Kasar haka? Sai ya ce, “Saboda wadanda suke tare da shi ba su ba shi shawara kan abin da ya kamata  a ce sun ba Shugaban shawarar abin da zai yi wa kasa. Ya ce “Saboda gurguwa da muguwar shawara da suke ba shi ne suka  sanya kasa take cikin wani mayuwacin hali idan ka ajiye aiki ka bar su su ne za su ji kunya ba kai ba,” inji babban fadan.

Da ya juya kan tattalin arzikin kasa da halin da ’yan kasar nan suke ciki Shugaban Darikar Angalika mai kula da shiyyar Kudu maso Kudu ya ce, “Matsalar tsaro ta ta’azzara a kasar nan ana yawan kama mutane ana yin garkuwa da su domin neman kudin fansa, bugu da kari hatta mace mai juna biyu ba ta tsira ba daga hannun masu sace mutane suna yin garkuwa da su ba, bare a ce malaman addini. A nan Kudu kuma yawan ta’addanci da tsageranci sun yi katutu sun samu gindin zama.”

Ya kara da cewa, matasa yau a kasar nan suna nan zaune da yawa sun gama manyan makarantu da jami’o’i suna zaune a gidajen iyayensu, babu aikin yi kamata ya yi gwamnati ta samar musu da aikin yi.

Da ya juya kan shirin nan na samar wa makiyaya matsugunni da Gwamnatin Tarayya ta nemi  bullo da shi wanda ake kira “RUGA” ya ce ko kusa ba su yarda da shirin ba, a soke shi kwata-kwata.  “Ba mu yarda da dakatar da shirin kadai ba, a soke shi kwata-kwata kawai,” inji shi.

A karshe ya bukaci lallai gwamanti ta mayar da hankalinta wajen sake fasalin kasar nan domin a rika bai wa jihohin da suka mallaki arzikin albarkatun kasa da ke jihohinsu, su rika cin moriyar abinsu.