✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin kudin wutar lantarki

Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta sahale wa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DISCOs) damar  kara kudin wutar lantarki, saboda kamfanonin su…

Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta sahale wa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DISCOs) damar  kara kudin wutar lantarki, saboda kamfanonin su samu damar cike gibin kudaden wutar da suka sayar wa abokan huldarsu. Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata takarda da ta wallafa mai taken  “Karamin Karin Kudin Wutar Lantarki na 2016-2018 na dokar sake duba karin kudi na kamfanonin sayar da wutar lantarki ta shekarar 2015  (MYTO).  Sakamakon gyaran, karin kudin wutar zai kasance ne tsakanin Naira 4 zuwa Naira 60 a kan kowane kilowatt ga gidajen kwana.

Hukumar NERC ta ce “Abin da dokar ta kunsa ya hada da daidaita canjin da aka samu a karamin gyaran da aka yi a shekarar 2016 zuwa 2018 domin hasashen kudin da za a karba a shekaru masu zuwa da kuma kirdadon hasarar da ka iya aukawa kudin wutar lura da canjin da ake samu a bangaren kudin sai kuma kyale kudin wutar lantarki ya rika tafiya da yanayin da ake bi wajen rarraba wutar lantarki a kasar nan.”

Idan za a iya tunawa a shekarar 2018 kamfanonin rarraba wutar lantarki (Discos) sun shelanta asarar da suka tabka a lokacin da suka sayar da  wutar lantarki  Naira 80.88 a kan kowace kilowatt daya sannan suka sayar da ita ga abokan hulda a kan Naira 31.50 a kan kowane kilowatt, wanda hakan ya sa kamfanonin suka yi asarar Naira 49.38 a kan kowane kilowatt. Lura da bayanan da kamfanonin Discos suke da shi, ya sa hukumar take neman  a duba don kara kudin wutar lantarki  bayan shekara biyu saboda lura da dokar MYTO wacce take bayanin yin kari ko ragi ga kudin wutar lantarki duk bayan wata shida. Gyaran dokar da aka yi na karshe shi ne a cikin shekarar 2015. Daga shekarar 2015 zuwa yanzu ya kamata  a ce an dubi dokar akalla sau shida kamar yadda dokar ta yi tanadi.

Yanayin da yake sawa a yi kari ko ragi a kan dokar ya kunshi abubuwa kamar haka: yanayin kudaden musaya na kasashen waje ko darajar Dalar Amurka a kan Naira: sai kuma farashin iskar gas a kasuwar duniya (domin ana amfani da iskar gas wajen samar da wutar lantarki): sai kuma yanayin karuwa ko raguwar samun wutar daga tashoshi;  da tashin farashin kayayyakin amfanin yau da kullum. Tun cikin shekarar 2015 wadannan abubuwa suna ta tashin gwauron zabo saboda haka tun wancan lokacin Hukumar NERC tana cikin tsaka mai wuya wajen bayar da umarnin kan karin kudin wutar. Shin hukumar tana dari-darin fushin kungiyoyin kwadago ne ko kuma tana tsoron zaben 2019. To ko ma mene ne Hukumar NERC ta yi karin kudin wuta saboda zabe ya zo ya wuce. Abin tsoron shi ne daga yanzu kudin wutar lantarki ka iya karuwa a kowane lokaci kuma a kai-a kai.

Abin takaicin shi ne abu ne mai wahala ga Hukumar NERC ta yi karin haske a kan dalilin tsadar samar da wutar lantarki domin ’yan Najeriya ba za su yarda da wannan dalili ba domin wutar ba ta samuwa daga kamfanonin Discos. Sabon karin da aka samu daga Naira 24 zuwa Naira 31 a kan kowane kilowatt ga kowane abokin hulda a cikin Abuja, wanda hakan ya sa aka samu karin Naira shida a kan kowane kilowatt. Sannan dokar nan ta kudin wutar lantarki a kauyuka da birane  babu daya daga cikin kamfanoni Discos 11 da yake aiki da ita. Dokar ta yi tanadin wadanda suke zaune a birane kudin wutarsu zai fi na takwarorinsu na karkara yawa. Birane za su biya kudi sama dana kauyuka kudin farko sai ya cike gurbin na biyu. Don haka muna kira ga Hukumar NERC ta umarci dukkan Kamfanoni Discos su fara amfani da wannan doka tunda har hukumar ta yi shelar karin kudin wutar lantarkin. Hukumar NERC ta ce Discos suna tafka asara wanda shi ne babban dalilin da ya sa aka yi karin kudin wutar. Amma gaskiyar zancen ba haka yake ba domin dalili ne na son kai kawai. Hasarar tana aukuwa ne dalilin rashin samar da isassun mitoci  ga gidajen jama’a. Idan har kamfanonin Discos suka samar da mitoci zai zama mafi sauki wajen karbar kudin daga gidajen jama’a. Koda an samar da mitocin ga mutane ita kuma wutar da ake samarwa ba ta isa dole matsala tana nan. Wannan shi ne babban kalubale ga Hukumar NERC.

Baya ga rashin isassun mitoci, akwai kayyayakin hukumar da suka lalace ko suka yi kadan kamar wayoyin manyan layuka (higih tension) da turaku da taransufomami, ya kamata a samar da isassu kuma nagartattu. Saboda haka muna kira ga Hukumar NERC da kamfanonin rarraba lantarki (Discos) su fara gyara matsalolinsu kafin su yi karin kudin lanatarki. ’Yan Najeriya ba za su ki biyan kudin wutar lantarki ba muddin sun amfana daga gare ta.