Da Dumi Dumi

Karin masarautu barnata dukiyar Kano ne – Abba Gida-Gida

Dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Injiniya Abba K. Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya bayyana  cewa wadannan  karin masarautun da Gwamnan Kano Dokta Abdllahi Umar Ganduje ya yi a matsayin wani shiri ne da wasu makiya jihar suka shirya da nufin tarwatsa lalitar gwamnatin jihar ta kano.

Dan takarar gwamnan ya yi wannan kira ne a lokacin da yake buda baki tare da wasu ‘yan kungiyoyin sufuri a Jihar Kano.

Abba K. Yusuf ya zargi Gwamna Ganduje da daukar abin da ba shi da Muhimmanici, domin kirkiro wadanan masarautu ba shi ne abin da al’ummar jihar kano suke bukata ba, a yanzu, hakazalika sauke manyan  sakatarori da kuma cin zarafin malaman addini a jihar duk wannan bai dace ba. Yace a dai dai lokacin da al’ummar jihar kano suke da bukatar a bunkasa  abubuwan ci gaba a Jihar, irin su ginin makarantu , asibitoci samar da ruwa da kuma abubuwan more rayuwar al’umma, amma kash  sai ga shi makiyan jihar sun kirkiri abin da zai zama karin nauyi ne, ga tattalin arzikin gwamnatin jihar ta kano.

Dan takarar Gwamnan ya kara da cewa “Mun sami labarin yadda Gwamna Ganduje  yake shirin kwasar wasu miliyoyin kudi don gina fada ga masarautun da aka kirkiro, tare da sayen motocin sarauta ga sabbin sarakunan hudu  da aka kirkiro, bayan hakan na zuwa a daidai lokacin da iyayen yara ba sa iya biya musu kudin makaranta, asibitoci babu magunguna, ga miliyoyin almajiran na ta gararamaba akan tituna,basu da gurin kwana mai kyau, “Don haka ina jan hankalin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje  da cewa abin da yake yi bai dace ba” a Jihar da take da yara sama da miliyan uku wadanda ba su iya zuwa makaranta  ga matasa sama da miliyan hudu da ba su da aikin yi suna zaman kasha wando, to kamata ya yi a bawa matasan nan, aiyukan yi ko koyar da su sana’oi.

ADVERTISEMENT
Share