✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin mutum 11 sun warke daga Coronavirus a Legas

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da cewa an sallami mutum 11 daga cibiyar killace masu cutar coronavirus da ke Yaba a jihar bayan…

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da cewa an sallami mutum 11 daga cibiyar killace masu cutar coronavirus da ke Yaba a jihar bayan sun warke.

Gwamnan ya kara da cewa, masu dauke cutar da aka sallama akwai biyu mata sai kuma tara maza. Sai da aka yi masu gwaji sau biyu aka tabbatar sun warke ba sa dauke da cutar.

”Ina son na yi amfani da wannan damar na gode wa jami’an lafiya da sauran ma’aikatan kiwon lafiya da wasu kwararru wajen ganin an dakile yaduwar wannan cutar.” In ji Gwamnan.

Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka Ta Najeriya, NCDC  ta ce yanzu haka an sallami mutum 20 da suka warke daga cutar Coronavirus a Najeriya.