Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Karin mutum hudu sun warke daga Coronavirus a Legas

Karin mutum hudu sun warke daga Coronavirus a Legas

Gwamnatin jihar Legas ta sake sallamar karin mutum hudu da suka warke daga cutar Coronavirus a jihar.

A sanarwar da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya fitar a shafinsa na twitter ya shaida cewa, mutum uku daga cikin mutanen da suka warke mata ne ragowar dayan namiji ne, ya ce dukkaninsu sun warke an kuma sallame su a yau Juma’a.

Ko a ranar Alhamis ma gwamnatin jihar ta bada sanarwar sallamar mutum 11 da suka warke daga cutar.

A ‘yan kwanakin nan ne Kwamishinan lafiya a jihar Legas Farfesa Akin Abayomi, ya bada tabbacin cewa majinyata cutar Coronavirus a Legas na murmurewa sosai kana babu alamar mutuwa a tare da su.