Da Dumi Dumi

Karin ‘yan Najeriya sun dawo daga kasashen waje

'Yan Najeriyan da suka dawo daga kasashen ketare saboda gudun cutar coronavirus
'Yan Najeriyan da suka dawo daga kasashen ketare saboda gudun cutar coronavirus

Karin ‘yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje sun sake dawowa gida yayin da ake ci gaba da kokarin yakar cutar coronavirus a fadin duniya.

Rukunin ‘yan Najeriyan sun sauka na a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Asabar, inda aka tantance su. 

Daga nan an killace su na tsawon kwanaki 14 domin tabbbatar da ba sa dauke da cutar coronavirus, kamar yadda doka ta tanada.

Jami’an hukumomin lafiya da suka haka da ma’aikatar lafiya ta tarayya da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa da jami’an hukumar shige da fice ne suka tarbi mayan bakin.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya