✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kariya daga ciwon zaizayewar kashi

A gobe Asabar ne ake bikin zagayowar ranar ciwon zaizayewar kashi a duniya. A irin wannan rana a ko’ina a duniya ana fadakar da jama’a…

A gobe Asabar ne ake bikin zagayowar ranar ciwon zaizayewar kashi a duniya. A irin wannan rana a ko’ina a duniya ana fadakar da jama’a musamman wadanda suka haura shekara 50 zuwa 60 kan sanin wannan matsala da yadda za su kiyaye aukuwarta ko rage mata kaifi. Duka maza da mata da suka haura wadancan shekaru suna cikin hadarin samun zaizayewar kashi, duk da cewa abin yakan fi kamari a mata saboda karancin wasu sinadarai bayan an manyanta.

Me ake nufi da zaizayewar kashi? Mun riga mun san jikinmu na da kasusuwa da dama da suke rike da shi. Kuma tun a kuruciya wadannan kasusuwa suke haduwa su fara girma su kuma yi kwari sosai idan an fara girma. To, bayan wannan kwari ne kuma kwatsam idan shekaru suka tunkaro maimakon kashi ya ci gaba da kara karfi sai kuma ya tsaya cak, a wadansu kuma daga nan sai ya fara zagwanyewa, kamar dai yadda gini ke rasa kwarinsa bayan wasu shekaru masu yawa. To wannan zagwanyewa ta sinadaran da suka hadu suka gina kashin ita ake kira ciwon zaizayewar kashi. Kuma akalla a cikinmu mutane sama da kashi 70 cikin 100 ne ke samun matsalar in dai tsufa ta tunkaro, sai dai kawai na wani ya fi na wani, wato a wadansu wadanda suka dauki matakan kariya da wuri, wato a kuruciya da wuya ma a gane akwai matsalar.

Idan kaddara ta sa sai an samu matsalar, to alamomin da mutum wanda ya ba shekara 60 baya, zai fara ji na cewa kasusuwa sun fara zagwanyewa sun hada da fara jin yawan ciwon jiki da alamu wadanda a gargajiyance akan danganta su da tsufa kamar tashi daga zaune zuwa tsaye da kyar, zama ma da kyar, tafiya da kyar, daga nan kuma sai a fara rusunawa wajen tafiya, wato idan ana tafiyar ba za a iya tsayawa kyam ba. A wadansu za a ga baya ya fara tankwarewa sun fara doro, wadansu kuma kafafuwansu su baude, ko sun yi gwame, masu tsayi su ga tsayinsu na raguwa sannu-sannu. Daga nan sai a rika faduwa idan ana tafiya, wadansu lokuta idan an fadi din, nan da nan za a samu karaya. Dama yawa-yawan abin da ke kawo karaya a masu yawan shekaru zaizayewar kasusuwan wurin ne.

Yaya za a kiyaye ko kuma a rage kaifin ciwon? To tun a kuruciya dai ake fara gina kashi, wato tun daga yarinta. Yara da suka samu abinci mai gina jiki kuma masu gina kashi kamar madara da hanta da kifi masu dauke da sinadaran calcium da bitamin D su suka fi kwarin kashi kuma su suke girma da kashi mai kwari wanda zai rage kaifin ciwon zaizayewar kashi. Sai yawan motsa jikin tun a kuruciya, shi ma yana taimaka wa lafiyar kashi. To idan aka girma a haka ana samun wadannan abinci a-kai-a-kai kuma ana yawan motsa jiki, to kasusuwan na kara kwari sosai kamar yadda bulon da ya sha siminti da ruwa ke kara kwari.

Sauran abin da za a yi la’akari da su idan ana so a kiyaye aukuwar matsalar su ne guje wa abubuwan da za su bata lafiyar kashi. Abubuwa masu bata lafiyar kashi kuwa sun hada da shan giya da busa sigari, sai kiba da shan kwayoyi masu sa kiba irin su kwayoyin sha-ka-fashe na steroids. To idan aka guji wadannan, aka kuma bi waccan shawara ta samar wa kashin sinadaran gina shi, to ko matsalar ta zo, za ta zo da sauki.

 

Mene ne amfanin rake a jikin mutum?

Daga Muhammad, Zuba

 

Amsa: Rake na cikin kayan itatuwa wadanda suke da ruwa da sukari da sinadarai irin su sodium da calcium, amma su sinadaran ba su da yawan da za a ce sun isa jiki ya yi amfani da su na rana daya ba, sukari ne ya fi yawa.

 

Mene ne amfanin dabino ga jikinmu?

Daga Muhammad Abubakar, Gwarinpa

 

Amsa: Dabino ma na daya daga cikin kayan ’ya’yan itatuwa masu sukari da sinadarai irin su potassium da magnesium masu yawa sosai wadanda idan aka ci kamar kwaya uku kacal za su iya isar mutum na aikin jikin rana guda.

 

Ni ina da matsalar kyasbi, na sha magani, na sha magani sai ya mutu, daga baya sai ya dawo. Ko mece ce shawara?

Daga Umar Mu’azu

 

Amsa: Ai ka san kyasbin iri-iri ne akwai wanda kwayar cutar fungus ke sa wa, akwai kuma na borin jini wato kamar canjin abinci ko na yanayi. Don haka dole sai an fara gano irin wanne ne kake da shi kafin a ba ka magani. Idan ka ga likitan fata zai iya taimakawa wajen bambance maka.

 

Wai da gaske ne idan mutum ya suma sai aka toshe hancinsa aka busa masa iska a baki zai farfado?

Daga Suraj Y. Ningi

 

Amsa: A’a, ba haka abin yake ba. Idan mutum ya suma ai numfashinsa ba daukewa yake ba idan ka lura. Idan ka ga numfashi ya dauke sai dai idan bugun zuciya ya samu. Don haka ko da an ga mutum ya suma ba a saurin busa masa iska a baki sai an ga ba ya numfashi. A bugun zuciya shi kuma abin da ya sa numfashin ke daukewa shi ne aikin zuciya na bugun jini zuwa kwakwalwa ya dan tsaya na wani lokaci. Tunda kwakwalwa ita ce wadda ke aika sako zuwa huhu don a yi numfashi. Ke nan da numfashi da aika jini sassan jiki ne ke tsayawa a lokacin da aka samu bugun zuciya, shi ya sa za ka ga idan hakan ta faru da numfashi da aikin zuciyar duka ake fara kokarin dawo da su a tare, ta hanyar busa iska a huhu (ta baki kamar yadda ka ce) don dawo da numfashi da kuma danna tsakiyar kirji don farfado da aikin zuciyar. Wannan shi ake kira taimakon gaggawa na wanda ya samu bugun zuciya.

Idan kana sha’awar koyon irin wannan taimakon gaggawa hanya mafi sauki ita ce za ka iya shiga shafin yanar gizo na YouTube domin kallon bidiyon yadda ake wannan taimako. Bahasin da za ka sa wurin da ake nemo bidiyon shi ne haruffan CPR.