Search
Subscribe
Karnuka 10 da bawan Sarki

Karnuka 10 da bawan Sarki

Karnuka 10 da bawan Sarki

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe.  Yaya karatu? Tare da fatan an koma makaranta lafiya. A yau na kawo muku wani labari mai taken: “Karnuka 10 da bawan Sarki” Labarin ya yi nuni ne ga aikin alheri na da ranarsa. A sha karatu lafiya:

Akwai wani Sarki yana da karnuka 10 masu tsananin cizo da mugunta . Yakan hukunta bayinsa da suka yi masa laifi da wadannan karnuka.

Ran nan wani bawansa ya yi subutar baki ya fadi wani abin da bai kamata ba sai ran Sarki ya baci. Ya ce lallai sai ya hukunta shi da wadannan karnuka.

Bawan Sarkin sai ya fadi gaban Sarki yana neman gafara ya ce: “Ya Sarkin garin nan na yi shekara goma ina yi maka bauta don Allah ka ba ni kwana goma kafin ka hukunta ni.” Sarki ya yarda.

Wannan bawan sai ya je wajen mai gadin wadannan karnukan ya ce ya taimaka ya bar shi ya kula da wadannan karnukan na tsawon kwana goma. Nan take ya amince. Daga nan bawa ya ci gaba da yi musu dawainiya ta hanyar yi musu wanka da ba su abinci da magani da kuma tsabtace musu wajen da aka ajiye su.  Wani lokaci ma yakan yi musu wasa ta hanyar jefa musu nama da kashi da yake sayo musu daga kasuwa da kudinsa ba tare da sanin Sarki ko ’yan gidan ba.

Mu kwana nan

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin