Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Karnuka ne suka cinye mamallakinsu da ya bace a Afrilu

An gano kasusuwan wani mutum mai suna Freddie Mack a Jihar Tekzas da ke Amurka, da ya bace tun watan Afrilu inda aka gano karnukansa da yake kiwo ne suka cinye shi suka bar kasusuwansa, kamar yadda wani jami’i ya sanar bayan gudanar da bincike.

Freddie Mack mai kimanin shekara 57, yana kiwon karnukan da suka 18, inda a waccan ranar karnukan suka fusata suka cinye shi tsaf, hatta kayan jikinsa da sumarsa ma ba su bari ba.

ADVERTISEMENT

Abin da karnukan suka bari kawai a jikin Freddie Mack, shi ne kasusuwan da ba su wuce tsawon inci biyu zuwa biyar ba.

Wadansu likitoci masu bincike bayan gwaje-gwajen kwayar halitta da suka yi (DNA) sun tabbatar da cewa ragowar kasusuwan da karnukan suka bari na Freddie ne.

ADVERTISEMENT

“Tunda muke ba mu taba samun labarin dabbar da ake kiwo ta cinye mutum kaf baki daya ba,” inji Mataimakin Shugaban Hukumar Tabbatar da doka ga ’yan kasa na ofishin Karamar Hukumar Johnson County Sheriff a Kansas, Mista Aaron Pitts.

Ya ce duk kasusuwan da suka rage an gatsa su kuma a karye suke.

Mista Freddie Mack, ya yi fama da rashin lafiya, kuma ba a tabbatar da a raye ne karnukan suka cinye shi ba ko sai bayan ya rasu ne saboda rashin lafiyar.

Magajin Garin Karamar Hukumar, Adam, ya ce sun yi jimamin rasuwar Freddie Mack, sannan suna mika sakon ta’aziyya ga iyalan Freddie Mack.

An sanar da bacewar Freddie Mack, tun a watan Mayu, inda  iyalan Freddie Mack suka ce ba su jin duriyarsa har zuwa tsakiyar watan Afrilu.

Jam’ai sun yi ta gudanar da bincike a gidan Freddie Mack, duk da yawan karnukan da suke cikin gidan amma daga bisani suka gano kasusuwan jikin Freddie Mack, a inda aka killace karnukan.

Bayan wasu kwanaki ana bincike, masu binciken sun gano wasu abubuwa ban mamaki da suke nuna alamar gashin kan mutum da ragowar sutura da kasusuwan mutum a kusa da inda aka ajiye karnukan.

Babban kashin da aka samu shi ne wanda aka aike da shi zuwa cibiyar binciken halittar dan Adam ta Jami’ar North Tedas inda a nan ka tabbatar da cewa kashin na Freddie Mack, bayan gwajin DNA.

Mataimakin Shugaban Hukumar ya ce, an kashe biyu daga cikin karnukan, sannan aka daure 13 saboda yanayin halittarsu, an kuma kai uku gwaji don bincike.

Jami’in ya kara da cewa, Freddie Mack yana lura da karnukansa matuka ta hanyar ciyar da su yadda ya dace tare da kaunarsu.

Ofishin Jami’an Hukumar sun ce, a shekarar 2017 Freddie Mack ya taba kiran wayar ofishin a kan ko za a iya samun wanda zai je ya lura da karnukansa, lokacin da yake jinya a asibiti