✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karuwa ta rasa ranta lokacin da ta dage sai a biyata ladanta

Wata karuwa ta gamu da ajalinta a lokacin da rikici ya barke a tsakaninta da farkanta kan kudin da suka amince zai ba ta, amma…

Wata karuwa ta gamu da ajalinta a lokacin da rikici ya barke a tsakaninta da farkanta kan kudin da suka amince zai ba ta, amma ya yi kememe ita kuma ta ce sai ya cika mata kudinta, lamarin da ya jawo rikici ya kaure a tsakaninsu ya daba mata wuka hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a yankin Surulere a ranar Larabar makon jiya. Ya ce fada ya kaure ne a tsakanin wanda ake zargin mai suna Babatunde Damilare da karuwarsa Elochukwu a gidan saukar baki na Edo da ke Surulere, bayan sabanin da suka samu a k n kudin da zai biya ta,  inda ya daba mata wuka lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarta. “An kai gawarta dakin ajiyar gawa domin ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da wanda ake zargin domin ya fuskanci shari’a,” inji Elkana.

Haka zalika rundunar ’yan sandan Legas ta kama wani mai suna Bunmi Adeyemi, mai shekara 35 da ake zargi da yi wa wata yarinya ’yar shekara biyra fyade a yankin Bariga. DSP Bala Elkana, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa zai kuma fuskanci shari’a yayin da aka garzaya da yarinyar cibiyar kula da lafiya ta Mirabul da ke Ikeja inda ake kula da lafiyarta.