Da Dumi Dumi

Karuwar garkuwa da mutane ta harzuka ’yan Najeriya

Gwamna Nasiru El-Rufa’i a wurin da masu garkuwa da mutane suka tsare shekarajiya Laraba
Gwamna Nasiru El-Rufa’i a wurin da masu garkuwa da mutane suka tsare shekarajiya Laraba

Karuwar garkuwa da mutane don karbar kudin fansa ta harzuka ’yan Najeriya inda suka nemi gwamnati ta dauki lamarin a matsayin wanda ke bukatar daukin gaggawa.

Aminiya ta gano masu garkuwa da mutanen da a baya sukan kai farmaki da dare a hanyar Abuja zuwa Kaduna, yanzu sun fara fitowa da rana-tsaka ba kunya ba tsoro suna kai hari ga jama’a a hanyar wadda ta hada Abuja da jihohin Arewa ta Yamma.

Daya daga cikin munanan harin takama da masu garkuwa da mutanen suka kai shi ne na shekaranjiya Laraba inda suka tare hanyar da misalin karfe 3:30 na rana a kusa da kauyen Akilbu da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna lamarin da ya tilasta wa masu wucewa tsayawa suna hangen yadda masu garkuwar ke yin artabu da wadanda tsautsayi ya auka musu.

A daidai lokacin ne Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i a hanyarsa ta zuwa Abuja da ayarinsa ya tarar da masu motoci tsaitsaye, suna neman agaji ganin yadda masu garkuwan suka tare hanyar.

Kakakin Gwamna El-Rufa’i, Mista Samuel Aruwan ya ce, a daidai lokacin ne Gwamnan ya umarci jami’an tsaron da suke tare da shi su rufar wa masu garkuwa da mutanen, inda nan take suka fatattaki garkuwa da mutanen suka shiga daji suka tsere.

ADVERTISEMENT

“Bayan jami’an tsaro sun yi nasarar fatattakarsu sai Gwamna El-Rufa’i ya umarci a kai wadanda suka ji rauni asibiti mafi kusa,” in ji Aruwan.

Wani ma’aikacin Kamfanin Daily Trust a hanyarsa ta zuwa Abuja a shekaranjiya Larabar ya ce da misalin karfe 4:15 an nuna masa wurin da masu garkuwa da mutane suka tare hanya a kauyen Kurmin Kare da ke kusa da titin jirgin kasa. Ya ce ya ga dimbin motoci a yashe da hakan ya nuna masu garkuwa da mutanen sun kama mutane da dama a yayin harin. Daga nan ne ma’aikacin namu ya ga yadda motocin ’yan sanda suna yin sintiri a daidai wurin da abin ya faru ba tare da nasarar kama ko ceto wani daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ba.

Haka a babbar hanyar fita garin Kaduna an ga wasu manyan motoci biyu sun yi karo da juna a kokarin kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane, inda hakan ya sa hanyar ta cunkushe kafin a samu nasarar kawar da motocin daga hanyar.

Wani mazaunin garin Kurmin Kare mai suna Lukman ya shaida wa Aminiya cewa kafin masu garkuwa da mutanen su tare hanyar, sai da suka yi garkuwa da wadansu manoma a gonakinsu.

Ya ce a yanzu masu garkuwa da mutanen ba manyan mutane ne kadai suke nema ba, suna yin abin nan ne da ake kira ‘kan mai uwa da wabi,’ inda duk wanda tsautsayi ya fada masa, to sai buzunsa.

’Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 3 a Kaduna

A wani labarin kuma a shekaranjiya Laraba ce da misalin karfe 5:45 na safe masu garkuwa da mutane su biyar suka yi yunkurin sace wadansu ma’aikatan Kamfanin Mothercart Limited da ke Mando, Kaduna.

Rahotanni sun ce maharan sun harbi ’yan sanda biyu da ke gadin kamfanin kuma daya daga cikinsu ya rasu a lokacin da aka kai shi asibiti.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Ohah Sunny ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da yake hira da manema labarai.  Ya ce, wadansu mutane dauke da bindigogi sun shiga harabar Kamfanin Mothercart suka rika yin harbin kan mai uwa da wabi, wanda hakan ya sa suka harbi ’yan sanda biyu da ke gadi a wurin.  Sai dai daya daga ciki ya rasu bayan an kai shi asibiti yayin da dayan yake jinya.

Ya kara da cewa ’yan sandan sun harbe uku daga cikin maharan a musayar wuta kafin sauran su ranta a na-kare dauke da miyagun raunuka. “A lokacin ba-ta-kashin jami’anmu biyu Sufeto Bijimi Maiyaki da Saje Kabiru Shu’aibu da ke karkashin rundunar tsaro ta Operation Yaki sun samu rauni, inda aka garzaya da su asibitin sojoji na 44 don yi musu jinya. Sai dai daya daga cikin jami’an ya rasu yayin da aka sallami dayan bayan an yi masa magani,” inji shi.

Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya yaba wa ’yan sanda game da nasarar da suka samu ta dakile garkuwar da aka so yi da ma’aikatan Kamfanin Mothercart da ke Kaduna.

A ranar Lahadin da ta wuce ma, an samu labarin yadda aka yi garkuwa da mutum 12 masu sana’ar sayar da itace a wani gari da ake kira Dagafada a Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.  Rahotanni sun ce al’amarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na safe.

A ranar Alhamis ta makon jiya ma, an samu labarin yadda wadansu ’yan bindiga a yankin Rigasa a Jihar Kaduna suka shiga gidan wani Abdul’azeez suka kashe shi, sannan suka yi awon gaba da matarsa mai shayarwa.

Wannan ne sa ya al’umma suka fara harzuka inda suka nemi gwamnati ta gaggauta yin wani don kawo karshen wannan bala’i ko kuma su fara tunanin daukar mataki.

Karuwar garkuwa da mutane ta harzuka ’yan Najeriya

Jama’a da dama suna cikin fargaba a Kogi

Jama’a a kauyuka da dama a Jihar Kogi suna rayuwa cikin fargaba sanadiyyar karuwar annobar garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Daga cikin kauyuka da garuruwan da suka fi zama cikin fargaba akwai Koton Karfe da yankin Obajana da Kabba da yankin Ajegwu zuwa Idah da yankin Ajaokuta da Adogo da kuma yankin  Itakpe zuwa Okene.

Majiyarmu ta gano cewa, fargabar garkuwa da mutane tana kawo nakasu a harkokin tattalin arziki.

A Unguwar Iraki da ke hanyar Kogi zuwa Koton Karfe, mai unguwar Idris Salihu ya ce, jama’ar unguwar suna zaune cikin zaman lafiya da ingantaccen tsaro, amma a wata uku da suka wuce, sai aka samu bullowar annobar garkuwa da mutane a yankin.

Idris Salihu, ya ce kwanakin baya masu garkuwa da mutane sun sace wani mazaunin unguwar mai suna Malam Yunusa Zaga lokacin da yake hanyar shiga unguwar.

Idris, ya ce bayan garkuwar da aka yi da mutumin, mutanen da suke garkuwar sun dawo suna yunkurin kama wadansu mutanen unguwar, amma ba su yi nasara ba sanadiyyar dakile shirinsu da ’yan bangar unguwar suka yi.

Shugaban ’yan bangar Unguwar Iraki, Zakari Hussain, ya ce matsalar garkuwa da mutane da fashi da makami ta zama babban kalubale da ke addabar jama’ar yankunan a yanzu.

Shugaban Riko na Karamar Hukumar Kogi-Koton Karfe, Malam Tanko Mohammed, ya ce karuwar garkuwa da mutan a karamar hukumar abu ne da suke kokarin dakilewa kuma gwamnati tana aiki tare da jami’an tsaro don magance kalubalen da ke damun jama’ar yankin.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kogi ta tabbatar da kama wadansu da ake zargi su ke yin garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Kogi-Koton Karfe da ke jihar.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kogi, Hakeem Busari ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a wata maboya lokacin da jami’an tsaro suka kai samame a yankin.

 ‘Babu wanda ya tsira daga masu garkuwa a Katsina’

A Jihar Katsina babu wanda ya wuce a yi garkuwa da shi, inda a cikin wata biyu da suka wuce, wadansu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da suka hada da Tsohon Daraktan Sashin Sirri na Sojojin Najeriya Manjo Janar UT Umar (mai ritaya) da surukar Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari, Hajiya Hauwa Yusuf sai kuma Sheikh Ahmad Suleiman tare da wadansu ’yan uwansa biyar da suke tare da shi.

Iyalan Lawal Kasko kuwa sai da suka biya kudin fansa kafin a sako ’ya’yansu da suka hada Amina mai shekara 11 da Abdullahi mai shekara 9 bayan sun kwashe kwana 23 a hannun masu garkuwa da mutanen.

Wadansu daga cikin hanyoyin jihar da ke cikin hadari saboda annobar garkuwa da mutanen sun hada da Jibiya zuwa Gurbin Baure zuwa Gusau da Sheme zuwa hanyar Kankara zuwa Faskari da Mara zuwa Gora zuwa hanyar Runka da kuma Safana zuwa Runka zuwa Batsari.

Sauran sun hada da Dutsinma zuwa ’Yantumaki zuwa Marabar Dan Ali zuwa Wawar Kaza zuwa Kankara da ’Yantumaki zuwa Maidabino da Kankara zuwa Pawwa zuwa Zango zuwa iyakar Zamfara da kuma Shimfidda zuwa Jibiya.

Mutum 227 aka yi garkuwa da su tun watan Disamba a Zamfara

Sakataren Riko na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Zamfara (ZEMA) Alhaji Aminu Umar ya bayyana wa wakilinmu a Gusau fadar jihar cewa, suna da rahoton an yi garkuwa da mutum 227 a jihar tun watan Disamba 2018 amma har yanzu ba a sako su ba.

Alhaji Aminu, ya ce an kashe mutum 408 tare da raunata mutum 126 da kuma lalata gidaje 248, kuma  wannan adadi zai wuce haka saboda rahoton da ba a kammala ba.

An samu rahoton cewa, akwai ’yan gudun hijira da adadinsu ya kai dubu 31 da 402 sanadiyyar hare-haren ’yan bindga da barayin shanu da suka addabin kauyuka da garuruwan jihar.

Mazauna jihar sun bayyana wa majiyarmu cewa, sun gargadi mutanen jihar a kan su kaurace wa wasu yankunan jihar da rana da daddare don gudun aukawa cikin tarkon masu garkuwa da mutanen.

Yankunan sun hada da Gusau zuwa Magami zuwa Dansadau da Kuceri zuwa Danjibga zuwa Keta zuwa Wanke da Kaura zuwa Namoda zuwa Moriki zuwa Shinkafi da Zurmi zuwa Jibiya a Jihar Katsina. Sun ce duk mai bin wadannan hanyoyi yana cikin hadari musamman da daddare, wannan bai hana a yi garkuwa da mutum ko da rana ne, kamar yadda wani mazaunin garin Aliyu Ashiru ya ce.

Mako biyu da suka wuce, an yi garkuwa da mutum 26, an kashe mutum biyu yayin da shida suka samu mummunan raunuka lokacin da masu garkuwan suka kai hari a wani masallaci a  Dansadau da misalin karfe 5:40 na asuba, masu garkuwan na bukatar kudin fansa Naira miliyan 20.

“Mawuyaci ne a rana ba a samu rahoton aikata garkuwa da mutane ba a Jihar Zamfara, wannan annobar ta zama ruwan dare. Hakan ya takaita zirga-zirgar jama’a musamman a yankunan karkara. Ko a babban birnin jihar ba ka tsira ba,” inji wani mazaunin jihar Sani Shu’aibu.

Abin da ya kamata gwamnati ta yi

Fitaccen malamin addinin Musulunci nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce garkuwa da mutane tana kara ta’azzara ce saboda matsalar tabarbarewar tattalin arziki. Malamin ya ce akwai rashin kokarin jami’an tsaro wajen gano tushen lamarin, “Jami’an tsaro sun gaza wajen gano bakin zaren wannan lamarin da ya addabi mutanen kasar nan. Yanayin kudin fansar da suke nema ya yi yawa kuma abin akwai takaici. Wadannan kudade sun fi karfin talaka. Ko ranar Talatar da ta gabata an yi garkuwa da wani mutum da na sani, kuma wai suna neman Naira miliyan 20. Don haka wannan lamarin yana damun kusan kowa a wannan jiha da kasa baki daya,” inji Dokta Gumi.

Game da yadda za a gano bakin zaren, malamin cewa ya yi dole ’yan Najeriya su hada hannu wajen yin wannan aiki, sannan ya kara da kira ga gwamnati ta cire siyasa ta dage wajen magance matsalar.

Wani direba mai suna Adamu Kilgo shi ma kira ya yi ga gwamnati ta magance lamarin domin yana kawo musu tarnaki wajen harkokin neman abincinsu, “Wani lokacin sai mutum ya rika tunanin wai me ke faruwa ne? Sai ka ga an yi garkuwa da mutum a kusa da inda ’yan sanda suke kuma babu abin da zai faru. Idan ka je ka fada musu halin da ake ciki, sai su fada maka cewa kawai ka je ka biya kudin fansa a sako maka dan uwanka lafiya,” inji shi.

Haka wadansu mutane da dama sun yi magana da wakilanmu, inda suka ce suna cikin tsoro da damuwa saboda harkokin garkuwa da mutane.

Shi ma Malam Abdul Sani cewa ya yi ya kamata a yi babban taron masu ruwa-da-tsaki domin shawo kan lamarin.

Rundunar Sojin Sama za ta taimaka wajen yaki da masu garkuwa da mutane

Rundunar Sojin Sama ta ce za ta taimaka wajen samar da tallafi a nata bangaren wajen bincike da yaki da lamarin ta sararin samaniya, inda ta ce za ta hada hannu da sauran takwarorinta wajen kawo karshen harkokin satar mutane.

Wata sanarwa da ta fito daga Kakakin Rundunar, Iya Kwamanda Ibikunle Daramola, ta ce wannan yana cikin ayyukan rundunar na hada hannu da sauran jami’an tsaron domin magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.

Ya ce wannan yunkuri ana yi ne musamman domin magance matsalar garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Ya ce Rundunar Sojin Sama ta kara nanata shirinta na aiki tare da ’yan sanda da jami’an tsaron sirri da sauran jami’an tsaro wajen binciko bayanan sirri tare da bayar da jiragenta dominn aiki ta sama.

Kwamanda Ibikunle ya ce Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Sadikue Abubakar ya bayyana haka ne  a shekaranjiya Laraba lokacin da ya gana da Sufeto Janar na ’Yan sanda, Muhammed Adamu da Daraktan Hukumar DSS, Yusuf Bichi a Babban Ofishin Rundunar da ke Abuja.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya