✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

karya ne ban mutu ba – Bukky Ajayi

Fitacciyar jaruma kuma kwararriyar ’yar jarida Bukky Ajayi ta karyata rade-radin da ake yi a kafafen sadarwa ta intanet cewa ta mutu a karshen makon…

Fitacciyar jaruma kuma kwararriyar ’yar jarida Bukky Ajayi ta karyata rade-radin da ake yi a kafafen sadarwa ta intanet cewa ta mutu a karshen makon da ya gabata.
Bukky ta yi watsi da yamadidin mutuwarta ne yayin da manema labarai suka tuntube ta ta wayar salula kan batun.
Ta ce, ‘karya ne ban mutu ba. Ina nan da raina cikin koshin lafiya. Na yi mamakin jin wannan labarI, mutane da yawa sun yi ta kira na suna gaya min cewa ana ta rade-radin cewa na mutu. Ban dauki abin da muhimmanci ba sai da ’yata da mijinta suka kira ni. Ku kyale su makiyana ne ba sa son ganina da rai kuma Allah Ya fi su, sai na cika burina a duniya. Ka san haka mutane suke ba sa son a zauna lafiya’.
Ta ci gaba da cewa ‘Ina so na yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga masoyana da ’yan’uwana su yi watsi da wannan jita-jita su ci gaba da yi min fatan alheri. Ina mika godiyata ga masoyana kuma ina mai tabbatar musu da cewa zan ci gaba da dadada musu kamar yadda na saba.’
A karshen makon da ya gabata an yi ta yada jita-jitar mutuwar Bukky ta kafafen intanet, inda wasu suka rika cewa ta mutu wadansu kuwa cewa suka rika cewa tana kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai.
Ita dai Bukky ta yi fice ne a fina-finan Nollywood da na Yarabanci kuma ta yi suna sosai dangane da gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin daban-daban.
Ta shafe shekaru da dama tana cin karanta ba babbaka a duniyar aikin jarida da fina-finai.
A kwanakin baya mutuwa ta rika yi wa jarumai da daraktoci da furodusoshi dauki-daidai, inda wasu daga cikin jarumai da dama ya duri ruwa saboda tsaron kada mutuwar ta ziyarce su.