✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karya ta jira wanda ya mallake ta sama da shekara a ofishin ’yan sanda bayan tsare shi

Wata karya mai suna Sheila, da ke garin Buenos Aires,  Babban Birnin  Kasar Ajentina, ta sanya miliyoyin jama’a cikin mamaki game da yadda ta yi…

Wata karya mai suna Sheila, da ke garin Buenos Aires,  Babban Birnin  Kasar Ajentina, ta sanya miliyoyin jama’a cikin mamaki game da yadda ta yi hakurin jiran wanda ya mallake ta a harabar ofishin ’yan sanda sama da shekara da tsare shi.

Rahotanni sun bayyana cewa, karyar ta kasance mai biyayya ga wanda ya mallake ta don haka ta yi zaman jiransa a ofishin ’yan sanda na yankin 25 de Mayo, daya daga cikin yankunan da ke birnin Buenos Aires a Ajentina. Bayan an saki mai ita daga tuhumar da ake yi masa a ofishin ’yan sandan, sai karyar ta ci gaba da bin sa kamar yadda ta saba. Sai dai abin mamaki tun lokacin da ’yan sanda suka kama mai karyar ko sau daya ba ta taba barin harabar ofishin ’yan sandan ba.

Ba a dade da tsare wanda ya mallaki karyar ba, ’yan sandan suka fahimci cewa, karyar tana jiran wanda ke tsare a ofishinsu ne, daga nan suka fara kawo wa karyar abinci. Da farko sun yi kokarin korar karyar daga harabar ofishinsu amma daga bisani sai karyar ta fara kwana a cikin ofishin idan dare ya yi, wani lokacin  har rakiya take yi  ’yan sandan idan za su fita aiki, idan ta kamala rakiyar za ta dawo ofishin ta ci gaba da jiran wanda ubangidanta.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan sandan,  Juan Jose Martini, ya bayyana wa kafar labarai ta Tucumanalas7 News cewa, tun ranar da aka tsare wanda ya mallaki Sheila, take ofishin ’yan sandan ba tare da ta bar harabarsa ba, saboda sabon da ta yi, hakan yake sa tana bin ’yan sanda zuwa wuraren aikinsu, wannan ya nuna karyar tana yi wa jami’an da suka tsare mata maigida rakiya saboda sabo. Karya Sheila tana da kimanin shekara 4 zuwa 5.

’Yan sanda sun bayyana gamsuwarsu da yadda karyar take nuna soyayya da biyayya ga wanda ya mallake ta, ta yadda take kwana kusa da inda yake tsare lokaci zuwa lokaci.

Watanni kadan da suka wuce, karya Sheila ta fuskanci wani mafadacin kare inda har sai da ta yi jinya a asibitin dabbobi, kuma ’yan sandan ne suka kai karyar asibitin har sai da ta yi kwana 15 a asibitin. Ofishin ’yan sandan ne ya biya kudin jinyar karyar. Bayan karyar ta warke ta dawo ofishin ’yan sandan don ci gaba da jiran mai ita.