Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Karyewar gada ta yi ajalin daliban Jami’ar Tafawa Balewa 4

Wata gada da ta karye a ranar Litinin 05/08/2019 ta wannan makon da misalin karfe 11:30 zuwa 12:00 na dare a cikin jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ATBU da ke Bauchi ta yi sanadiyyar rasuwar mutum hudu yayin da wasu mutum bakwai suka jikkata bayan an shafe sa’o’i ana ruwan sama.

A yanzu haka hukumomin makaranta sun dakatar wasu ayyukan jami’ar yayin  da ake ci gaba da lalubo wadanda suka bace  sanadiyyar karyewar gadar, Shugaban Jami’ar Mohammed Ahmed Abdulazeez, ne ya bayyanawa manema labarai hakan, inda ya ce gadar jami’ar ta karye ne a cibiyar jami’ar da ke Gubi.

ADVERTISEMENT

Daliban da suka jikkata a yanzu haka suna asibitin koyarwa na jami’ar Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke cikin garin Bauchi.

ADVERTISEMENT