✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin 2021: Noma da Arewa maso Gabas na bukatar kudade —Monguno

Mai tsawatarwar Majalisar Wakilai ya jaddada muhimmancin a kara kason bangarorin a kasafin 2021

Mai tsawatarwar Majalisar Wakilai Mohammed Tahir Monguno ya bukaci bangaren zartarwa ya ware karin kudade ga bangaren noma a kasafin badi a matsayin noma na kashin bayan tattalin arzikin Najeriya.

Honorabul Monguno ya kuma bukaci a ware karin kudade domin farfado da tsaro ta abubuwan jin dadin rayuwa a yankin Arewa maso Gabas mai fama da matsalar tsaro.

Monguno ya ce kara wa yankin Arewa maso Gabas kudade a kasafin ya zama wajibi idan aka yi la’akari da irin barnar da rikicin Boko Haram ya yi wa abubuwan more rayuwa a yankin.

Dan Majalisar ya ce yin hakan shi ne matakin farko na farfado da yanayin abubuwan more rayuwa a yankin da ya shafe sama da shekara 11 yana fama da rikicin Boko Haram.

Yayin tsokacinsa a lokacin karatu na farko da majalisar ta yi wa kasafin na tiriliyan N13.08 Monguno da ke wakiltar mazabar Marte/Monguno/Nganzai ya ce a gwamnatocin baya sun yi wa yankin kwange a kasafin kudi.

Ya kuma bukaci gwamnati da ya mayar da hankali wajen bunkasa bangaren noma, wanda ya ce ke samar da kashi 70 na ayyukan yi a Najeriya da ma kasashen Afirka.