✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin 2021: Majalisa ta bukaci a kara wa bangaren tsaro kudi

Dole a bullo hanyoyin samar wa bangaren tsaro kudaden bayan wanda ake yin kasafi

Majalisar Wakilai ta bukaci a kara wa bangaren tsaro bayan wanda aka ware masa a kasafin 2021.

Shugaban Kwamitin Majalisar kan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Abdulrazak Namdaz ya ce biliyan N840.56 da aka ware wa bangaren daga cikin Naira tiriliyan 13.08 na kasafin 2021 ba za su iya sayen makamai da gudanar da ayyukan samar da tsaro a sassan kasar ba.

Da yake kira a bullo da hanyoyin samar da kudaden tsaro baya ga kasafin kudi, Namdas ya ce, “Mu jingine ware wa bangaren tsaro kudade daga kasafin kudi; Babu kasar da ke amfani da kasafinta wajen biyan bukatun bangaren.

“Na san gwamantin na bayar da abin da za ta iya ne kuma ba za ta ba bangaren dukkannin kudadenta ba saboda sauran bangarorin ma suna bukata.

“Ba ina nufin cewa abin da ake ware wa bangaren ba daidai ba ne. Akwai kudurin dokar da aka yi wa karatu na biyu a Majalisar da ke jiran karatu na uku” inji shi

Idan ba a manta ba Majalisar Wakilai ta kammala karatu na biyu kan kudurin dokar kafa “Asusun Tallafa wa Rundunar Sojin Najeriya” wanda Honorabul Babajimi Benson da wasu mutum shida suka gabatar.