✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin Kudi: Za a kashe wa tsofaffin shugabannin Najeriya Naira Biliyan 2.3

Gwamnatin tarayya zata kashe wa tsofaffin shugabannin Najeriya da mataimakansu, dama manyan hafsoshin mulkin soja, kudade sama da Naira biliyan 2.3, a kasafin kudin shekarar…

Gwamnatin tarayya zata kashe wa tsofaffin shugabannin Najeriya da mataimakansu, dama manyan hafsoshin mulkin soja, kudade sama da Naira biliyan 2.3, a kasafin kudin shekarar 2020.

Wannan kudade da za a kashe na cikin daftarin kasafin kudin shekarar 2020, wanda Shugaba Buhari ya gabatarwa majalisun tarayya, wanda ke nuna cewa an ware kudin ne da yakai Naira biliyan 2.3, domin kula da walwalar tsofaffin shugabannin Najeriya.

Idan majalisar ta amince da kashe wadannan kudade, ya zamana za a kashe wa tsofaffin shugabannin Najeriya kudin da ya kai Naira biliyan 22.2 a cikin shekaru 16, gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara ware wadannan kudaden ne a cikin kasafin kudin shekarar 2005, don gudanar da walwalar tsofaffin shugabannin Najeriya.