✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin kudin bana:-`Yan majalisar wakilai munafunci dodo ya kan ci mai shi

A lokacin da masu ruwa da tsaki na jam`iyyar APC da ma masu yi wa jam`iyyar fatan alheri suka dukufa wajen ganin sun sasasanta tare…

A lokacin da masu ruwa da tsaki na jam`iyyar APC da ma masu yi wa jam`iyyar fatan alheri suka dukufa wajen ganin sun sasasanta tare da kawo karshen rikicin da ake fama da shi tsakanin bangaren Zartarwa da na Dokoki a cikin Majalisar Dattawa, tun bayan da Hukumar kula da da`ar ma`aikata wato CCB ta gurfanar da Shugaban Majalisar Dattawa Dokta Bukola Saraki gaban Kotun da`ar ma`aikata wato CCT a kan tuhumar yin almundahana wajen bayyana kaddarorinsa tun zamanin yana gwamnan jiharsa ta Kwara tsakanin shekarun 2003  zuwa 2011. Ba a kai ga shawo kan matsalar ba balle kammala shari`a ba, sai kuma ga Hukumar yaki da ta`annati da kudin jama`a ta EFCC, ta  kuma gurfanar da shugaban Majalisar Dattawan Dokta Saraki da mataimakinsa Sanata Ike Ekweremadu da wasu ma`aikatan Majalisar uku ciki kuwa har da tsohon Akawun Majalisun Alhaji Salisu Maikasuwa, bisa zargin sun canja wasu sassa na dokokin gudanar da harkokin Majalisar Dattawan, gyaran da ake zargin shi ya zama budi a kan yadda aka zabi Sanata Dokta Sanata Saraki da sauran shugabanni  na Majalisar Dattawan ta takwas (8).
Ana cikin neman mafita a kan waccan matsala da wasu masu goyon bayan shugabancin Dokta Saraki da makarrabansa suke zargin tamfar bita da kulli shugabancin jam`iyyar APC da ofishin shugaban kasa suke yi wa shugaban Majalisar Dattawan, bisa ga bijire wa umurnin da ta yi wa Majalisun Dokokin biyu, ta  Dattawan da ta Wakilai a kan wadanda za a zaba. Inda yayin da Sanata Saraki ya bijire wa umurni jam`iyyarsu ta APC ya samu nasara da taimakon `yan jam`iyyar PDP, tsohuwar jam`iyyarsa. Yayin da Mista Yakubu Dogara ya yi jirwaye mai kamar wanka a kan yadda jam`iyyarsu ta APC ta ce ga wadanda za a zaba, duk kuwa da jam`iyyar ba ta samu yadda take so ba. Wancan kin bin umurni ake zargin bangaren zartarwa ta yi amfani da shi ta maka shugaban majalisar dattawan da mataimakinsa kotu. Tuni dai jam`iyyar ta APC da shi kansa ofishin shugaban kasa suka nisanta kansu kan suna da hannu a kan halin da shugabancin Majalisar Dattawan ya samu kansa.
Yanzu kuma abin da ya kunno kai a cikin Majalisar Wakilai ta tarayya, wanda na Majalisar Dattawa yake neman zama wasan yara, don kuwa a tashi daya zai yi awon gaba da dukkan shugabanni da wasu shugabannin kwamitoci majalisar su 12, shi ne irin koke-koken da tsohon Shugaban Kwamitin kasafin kudi na Majalisar Alhaji Abdulmumin Jibrin Kofa ya mika wa Hukumar EFCC da ta ICPC, a kan yana zargin Shugaban Majalisar Wakilan Mista Yakubu Dogara da mataimakinsa, Yusuf Suleiman Lasu da bulaliyar Majalisar, Alhaji Alhassan Ado Doguwa da shugaban marasa rinjaye, Leo Ogar da Shugaban Kwamitin Babban Birnin Tarayya, Haruna Hemba da shugaban Kwamitin Ilimi mai zurfi, Zakari Mohammed da Shugaban Kwamitin kiwon Lafiya Chike Okafor. Sauran wadanda Jibrin ya hada da sunayensu a cikin koken nasa sun hada da Shugaban Kwamitin hasken wutar lantarki, Dan Asukuo da na kwamitin Sufurin jiragen ruwa, Mohammed Bago da na harkokin `yan sanda, Haliru Jika da na harkokin cikin gida, Joshua Adam Jagaba da na Kwamitin Harkokin Majalisar, Nasiru Baballe Ila.
Zarge-zargen da Abdulmumin Kofa ya mika wa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da ta`annati da kudin jama`ar biyu, sun hada da azurta kansu ta haramtacciyar hanya da yin amfani da mukamansu a kan hanyar da ba ta dace ba, da cin amanar mukaman da suke rike da su da gudanar da rayuwa a kan abin da ya fi karfin albashi da alawus-alawus dinsu da kuma irin yadda suka caccanza sassa daban-daban na saka ayyuka da suka kai dubu biyu a cikin kasafin kudin banan, don cimma bukatarsu, zarge-zargen da ya ce lallai hukumomin biyu su yi bincike kuma binciken kwa-kwaf a kan wadannan mutane da ya zarga. Tuni dai Majalisar Wakilan ta dare gida biyu, masu goyon Kakakin Majalisar da makarrabansa suna ta nisanta su da zarge-zargen da ake masu, suna kuma cewa, Abdulmumin Kofa duk shi ya kitsa kare-kare da canje-canjen da aka yi a Kasafin kudin na bana. Yayin da a gefe daya, magoya bayan Abdulmmumin suke ta hura wutar cewa lallai duk abin da aka samu na ba daidai ba a kasafin kudin da masaniya da yardar su Kakakin Majalisar da wasu shugabannin wasu Kwamitocin Majalisar. Zuwa yanzu Kakakin Hukumar EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya tabbatar wa manema labarai a Abuja a cikin makon da ya gabata cewa, Hukumar ta karbi koke-koken Abdulmumin, tare da bayar da tabbacin cewa kamar kowane koke da a kan mika musu shi ma na Majalisar Wakilan za su duba shi da aniyar daukar duk matakan da suka kamata.
Wannan tonon silili da Abdulmumin ya yi  ga shugabanninsa da sauran takwarorisa bai rasa nasaba da irin yadda a ranar 21 ga watan Yulin da ya gabata, Shugaban Majalisar Wakilan Yakubu Dogara ya bayar da shelar sauke shi Abdulmumin daga kan mukaminsa na kwamitin kasafin kudi a majalisar, a bisa zargin irin rawar da ya taka cikin canje-canje da kare-kare da ma sauya wasu tanade-tanaden kasafin kudin na bana. daya daga cikinsu in ji Yakubu Dogara shi ne cusa gina kauyen yin fina-finai da za a sanya wa sunan Shugaba Buhari a cikin karamar Hukumar Bebeji da ke cikin Jihar Kano, wato mazabar dan Majalisa Abdulmumin.
Maganar canjawa da kare-kare da ma sauya akalar kudin da ke cikin daftarin kasafin kudin kasar nan tunda aka dawo mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, ba wani sabon labari ba ne, balle ma ya zama laifi. A bana ne dai ya zama wani sabon labarin da har ya zama laifi. Don kuwa hakan kuwa ya yi ta faruwa ne a kan irin hadin bakin da a kan samu tsakanin `yan Majalisun Dokokin kasar nan, musamman shugabannin kwamitoci daban-daban da ma`aikatan gwamnati, musamman na ofishin shirya kasafin kudin gwamnatin tarayya. Amma a bana saboda Shugaba Buhari ya zuba idanu, shi ya sa ma ake samun wannan fallasa.    
Alal misali a bana akwai rahotanni masu karfi da suke tabbatar da cewa a kasafin kudin bana dan Majalisa Abdulmumi ya ware wa kansa ayyukan raya kasa har na sama da Naira biliyan hudu a mazabarsa, da ya yi aniyar gina katafaren kauyen shirya fina-finai da za a sanya wa sunan kauyen shirya fina-finan na Shugaba Buhari na sama da Naira biliyan uku. Sannan ya ware wa Shugaban Majalisar Yakubu Dogara sama da Naira biliyan uku don ayyukan mazabun, a tasa mazabar. Alhali a kan wannan kaso na ayyukan mazabu wasu `yan majalisar da suka kasance ya ku bayi da kyar wasu suka samu Naira miliyan 40 don ayyuka a mazabunsu.            
Daga rigimar da take neman cinye shugabannin majalisun dokokin na kasa biyu da makarrabansu ko `yan kanzaginsu, ba abin da take nuni akai da ya wuce ta `yan magana “Munafunci Dodo ne ya kan ci mai shi,”  ma`ana a lokacin da ake cikin munafunci ba ka jin akasarin `yan majalisun kamar yadda ake jinsu a yau. Ba kuma abin da zai yi maganin haka, mulkin dimokuradiyya ya inganta da ya wuce a bi ka`ida, tare da kamanta adalci a dukkan abin da za a yi cikin gudanar da mulki.