Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kasar Myanmar ta saki ’yan jaridar da ta kama

‘Yan jarida biyu da aka sako

A ranar Talatar da ta gabata ce aka saki wadansu ’yan jarida biyu na Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters da aka kama a kasar Myanmar, bisa zargin karya dokar sirrin bayanai, da aka kafa kafin kasar ta sami ’yancin kanta daga mulkin mallaka.

Wa-Lone da Kyaw Soe Oo na daga cikin dubban fursunoni da Shugaban Kasar Myanmar Wyn Myint ya yi wa afuwa a karkashin shirin afuwa na kowace shekara, da hukumomin kan tsara don murnar shagulgulan sabuwar shekarar gargajiya da aka fara  daga ranar 17 ga watan Afrilu.

ADVERTISEMENT

Dandazon ’yan jarida ne suka tarbe su, lokacin da suka fito bakin kofar gidan yari mafi tsanani da ke birnin Yangon.

Wa Lone, ya ce a shirye yake ya ci gaba da aikinsa na jarida, ya kara da cewa, “Ai har na kosa in koma dakinmu na watsa labarai.” Kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

ADVERTISEMENT

A watan Satumba ne aka yanke wa ’yan jaridar biyu hukuncin daurin shekara 7 a gidan yari bayan daukar labarai da suka yi na irin gallazawar da sojojin kasar suka rika yi wa Musulmin Jihar Rakhine da ke Arewa maso Yammacin kasar ta Myanmar.

Lamarin ne ya tilasta wa dubban ’yan kabilar Rohingya yin gudun hijira zuwa kasar Bangladesh a shekarar 2017.