✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasar Yemen na neman agajin gaugawa

Kasar Yemen ta yi kira ga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Hukumar Bayar da Tallafin Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da su kara…

Kasar Yemen ta yi kira ga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Hukumar Bayar da Tallafin Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da su kara yawan ayyukan kawar da cutar kwalera a fadin kasar.

Ministan Kananan Hukumomi ta Yemen Abdurrakib Fetih ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran SABA ta kasar cewa suna kira ga hukumomin WHO da UNICEF da su kara yawan ayyukan tsaftace muhalli da tsaftace ruwan sha da kuma ayyukan da za su kawar da cututtuka.

Fetih, ya kara da cewa tsaftace muhalli da ruwan sha da makamantansu ne kawai za su rage yaduwar cututtuka a fadin kasar.

Ya jaddada cewa a yankunan da Houthis suka fi yawa ne cutar kwaleran ta fi tsanani, hakan ko ya faru ne saboda da rashin samun daman kai magani a yankunan.

A cikin shekara biyar dai da ake fama da rigima a Yemen, mutane da dama sun rasa rayukansu, kasancewar yadda kasar ta kasance cikin kasashe masu tsananin talauci a duniya.

Yadda da dai yunwa, da cutar kwalera, da kai hare-hare suka yi kamari a kasar, wannan ya sa al’ummar kasar na cikin wani mugun hali.