Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kasashen Afirka ta Yamma za su fara amfani da kudi na bai-daya

Kasashen Afirka ta Yamma sun sanya hannu kan takardar amincewa da fara amfani da kudin bai-daya mai suna ECO.

Amincewar ta biyo bayan taron da Kungiyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta gudanar a Abuja, Babban Birnin  Najeriya.

ADVERTISEMENT

Kasashen na ECOWAS sun kunshi Benin da Burkina Faso da Cape Berde da Kwaddibuwa da Gambia da Ghana da Gini da Gini-Bissau da Laberiya da Mali da Nijar da Najeriya da Senegal sa Saliyo da Togo.

A jawabin Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Najeriya, Alhaji Mustapha Suleiman ya ce kungiyar za ta tsara yadda za a fara amfani da kudin da sashen hada-hadar kudi da tsare-tsare na kungiyar.

ADVERTISEMENT

Sabon Shugaban Kungiyar ECOWAS, kuma Shugaban Jamhuriyyar Nijar, Mahammadou Issofou ya ce kasashen  da suka kammala shirin fara amfani da kudin na bai- daya za su fara daga watan Janairun badi, amma kasashen da ba su kammala shiri ba za su iya shiga shirin daga baya.

Sai ya roki shugabannin kasashen su maida hankali domin samun nasara ga abin da suka sa a gaba.