Daily Trust Aminiya - kasashen duniya sun yi amanna da Rowhani a matsayin sabon sh
Subscribe

kasashen duniya sun yi amanna da Rowhani a matsayin sabon shugaban kasar Iran

Shugabannin kasashen duniya sun yi murnar nasarar Hassan Rowhani, wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon da ya wuce, inda suke sa ran ganin Iran ta samu daidaito da sauran kasashe kan shirinta na nukiliya, inda za a tabbatar da hakikanin gaskiyar shirin har a aminta da shi. Mafi yawan kasashen duniyar sun bayyana Rowhani a matsayin malamin addini mai sassaucin ra’ayi.
“Abin da gwamnatina ta za ta bai wa fifiko shi ne kyautata dangantaka da makwafta, musamman kasashen da ke yankin tekun Fasha da kasashen Larabawa da ke da matukar muhimmanci, tare da ’yan uwanmu,” inji Rowhani. Don a cewarsa: “Saudiyya ‘yar uwa ce kuma makwafciya, wadda muke da dangantakar tarihi da al’adu da kuma kasancewarmu a nahiya guda.” Ya kuma bayyana wannan manufa tasa ne a wani taron ’yan manema labarai da ya kira, tun bayan da ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar. “Ina fatan ganin gwamnati mai jiran gado ta kyautata dangantakarta da makwaftanmu, wadanda suka hada da Saudiyya.” kasar Saudiyya, wadda suka samu sabani kan rikicin Siriya, inda Iran ke goyon bayan Shugaba Bashar Al-Assad, ita kuwa Saudiyya ke mara wa ’yan tawaye baya.
“Manufar dai a samu daidaito da kasashen da ke da kujera a Majalisar tsaro ta Majalisar dinkin Duniya, tunda al’amarin nukiliya ba za a iya warware matsalar ba tare da yarjejeniya ba,” a cewar Rowhani, da yake nuni da yake yin ishara kan kasashe biyar masu kujera a Majalisar tsaro ta Majalisar dinkin Duniya, tare da kasar Jamus.
Wannan nasara da sabon shugaban dan shekara 64 ya smau ana sa ran za ta warware matsalatar dangantakar kasar da kasashen Yammacin Turai, sai dai ya yi amfani da taron ’yan jarida na farko da ya gudanar, inda ya bayyana cewa kasarsa ba za ta dakatar da shirinta na bunkasa makamashin nukiliya ba.
Zababben shugaban kasar ya yi fafutika wajen shiga tsakanin kasrsa da sauran kasashen duniya da ke takaddamar kan shirin sarrafa makamashin nukiliya da kasar Iran ke yi.
Rowhani ya sha alwashin inganta dangantakar kasarsa da Amurka, wadda suka yanke hulda, tun bayan da dalibai masu ra’ayin Musulunci suka kwace ofishin Jakadancin Amurka a shekarar 1979.
Sabon shugaban kasar ya samu gagarumar nasara tare da tallafin masu fafutikar kawo sauyi, inda dubban mutane suka yi tururuwa a kan tituna suna murnar nasararsa. Su kuwa manyan kasashen duniya syuke yin takatsantsan wzajen samun tabbaci.
Tun cikin shekarar 2006 Gwamnatin Tehran ke fafatawa da kasashe biyar masu kujera a Majalisar tsaro ta Majalisar dinkin Duniya, wadanda suka hada da Birtynaiya da China da Faransa da Rasha da Amurka, tare da Jamus (wadanda a Turance ake yi wa lakabi da P5+1), kan shirinta na sarrafa makamashin nukiliya. Saboda kasa cimma wata yarjejeniya da wadannan kasashe da aka ambata, shi yasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi fama da takunkumin tattalin arziki. “Barazana da takunkumi ba su yi tasiri ba,” a cewar Rowhani, a lokacin da yake ganawa da manema labarai. “kakaba takunkumi ba adalci ba ne, an jefa al’ummar Iran cikin wahala, alhali shirinmu na nukiliya al’amari ne wanda bai saba wa doka ba. Takunkumi ya saba wa doka, an kuma kakaba shi ne domin amfanin Isra’ila kawai,” a cewar mutumin da zai maye gurbin Mahmoud Ahmadinejad a farkon watan Agustan bana.
kasashen Yammacin Turai da Isra’ila sun dauka cewa wannan shiri ne da Iran ke yi don kera bom, amma a kodayaushe Tehran ta jajirce kan cewa shirinta na nukiliya na kyautata zaman lafiya ne.
Rowhani ya samu nasarar lashe zabe da kimanin kashi 50 cikin 100 na kuri’un da aka kada a ranar Juma’ar makon da ya wuce, inda aka samu rabuwar kai a tsakanin ’yan hamayya.
Ya bayyana wa magoya bayansa cewa zai iya kokarinsa wajen kawo sauyi, kan kammala wa’adin masu ra’ayin rikau karkashin gwamnatin Shugaba Mahmoud Ahmadinejad. “Da yardar Allah, wannan shi ne sharar fage wajen kawo sauyin da al’umma ke bukata a fannonin da suka hada da tattalin arziki da al’adu da zamantakewa da siyasa,” a cewarsa, inda ya yi gargadin cewa wadannan al’amura ba lokacin guda za a aiwatar da su ba, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.
Ya bayyana wasu sharudda game da dawo da dangantaka tsakanin kasarsa da Amurka, inda ya ce: “Amurka ba za ta yi mana katsalandan a cikin harkokin cikin gidanmu ba, ta kuma amince da ’yancin kasar Iran, tare da ikon mallaka nukiliya’ sannan ta daina yin dokokin karantsaye da tursasa mata,” inji shi.
Ita kuwa babbar jami’ar yin maslaha tsakanin Iran da kasashen Yammacin Turai, Catherin Ashton, ba za ta amince da alkawuran Rowhani ba. “Zan ci gaba da kira ga Iran ta zo mu yi aiki tare, don samar da tabbacin zaman lafiya kan shirinta na nukiliya,” inji ta.

texem
More Stories