✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kasashen duniya sun yi tir da kisan gillar da aka yi wa magoya bayan Mursi

kasashen duniya sun yi tur da kisan gillar da ake yi wa Misirawa, inda Amurka da Tarayyar Turai suka fito karara suka soki lamirin tashe-tashen…

kasashen duniya sun yi tur da kisan gillar da ake yi wa Misirawa, inda Amurka da Tarayyar Turai suka fito karara suka soki lamirin tashe-tashen hankulan da ake yi a kasar Masar, a daidai lokacin da aka yi wa magoya bayan Shugaba Mursi na Jam’iyyar Musulunci.
Fadar Gwamantin Amurka da ke Washington ta yi kira ga sojojin Masar, wadanda suka kawar da Gwamnatin Shugaba Muhammad Mursi da su yi takatsantsan, bayan sun kashe mabiyan Mursi mutum 55.
kungiyar ’yan uwa Musulmi ta Shugaba Mursi, ta yi kira da a yi wa gwamnati tawaye, sanadiyyar kisan gillar da aka yi wa ’ya’yanta. “Mun yi matukar damuwa kan yawan tashe-tashen hankula da ya baibaye kasar Masar. Mun yi suka da kakkausar murya kan duk wani tashin hankali ko masu tada zaune-tsaye,” A cewar Mai magana da yawun ma’aikatar cikin gida, Jen Psaki, kamar yadda ta bayyana wa manema labarai
“Daidaituwar al’amura a Masar da tsarin siyasa kan tafarkin dimokuradiyya na cikin hadari,” injita.
Shi kuwa mai magana da yawun fadar White House, Jay Carney, ya soki lamirin kiran da kungiyar ’yan uwa Musulmi “inda suka yi kiran tayar da kayar baya.”
Ya ce har yanzu Washington ba ta yanke huklunci kan cewa kifar da Gwamnatin Mursi da sojoji suka yi ko juyin mulki ne, kamar yadda ’yan uwan suke ikrari, ko kuma wannan wani yanki ne na juyin juya hali a kan gwamnatin da ta nuna gazawa, kamar yadda magoya bayansu ke ikirari.
Gwamnatin Amurka ta saba bai wa sojojin Masar taimakon Dalar Amurka bioliyan daya da rabi a kowace shekara, al’amarin da ake ganin za a iya dakatarwa, matukar aka tabbatar da cewa juyin mulki suka yi wa zababbiyar gwamnati. Sai dai Carney ya ce “al’amarin ba zai yui mana kyau ba” idan har muka yi saurin yanke tallafin, inda ya ce za a dauki lokaci kafin mu yanke hukunci ci gaba da bayar da tallafin na tsawon lokaci.