Da Dumi Dumi

Kashe Janar Soleimani: Najeriya ta shirya wa ba-zata

Shugaban ’Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu
Shugaban ’Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu

Babban Sufetan ’Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya umarci jami’ansa su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a sassan kasar nan sakamakon bayanan da ke da nasaba da kisan da Amurka ta yi wa Jagoran Sojojin Iran, Janar Kassem Soleimani.

A wata sanarwa da ya fitar, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeriya, Frank Mba ya ce, sun samu bayanan sirri da ke cewa, wadansu mutane na shirin tayar da kura ko  yin zagon kasa ga Najeriya bayan kisan Soleimani.

Sanarwar ta ce, an umarci Mataimakan Babban Sufeton ’Yan sandan Kasar nan da  Kwamishinonin ’Yan sanda su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a sassan kasar nan.

Babban Sufetan ya lashi takobin bayar da tsaro ga ’yan Najeriya da baki da ke zaune a kasar nan, yayin da ya gargadi masu tayar da kayar baya su kauce wa fantsama kan tituna.

Kisan da Amurka ta yi wa Janar Soleimani ya tunzura jama’a ga yin zanga-zanga a birnin Tehran da wasu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Juma’a, yayin da rahotanni ke cewa, ’yan Shi’a sun gudanar da makamanciyar wannan zanga-zanga a birnin Abuja.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya