Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Kashe Naira biliyan 19: APC ta jawo hankalin Gwamna Tambuwal kan siyasantar da bangaren ilimi

Kashe Naira biliyan 19: APC ta jawo hankalin Gwamna Tambuwal kan siyasantar da bangaren ilimi

Jam’iyar APC a Jihar Sakkwato ta jawo hankalin Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal kan yadda ta ce ya ya siyasantar da bangaren ilimi ta yadda malamai da ma’aikata a fannin ba sa jin dadin yadda abubuwa suke tafiya.

Jam’iyar ta ce tana son ta tunatar da Gwamnan cewa ya dauki rantsuwar zai jagoranci jama’ar Jihar Sakkwato ba tare da sanya son rai ba, kan haka akwai bukatar ilimi ya samu ci gaba mai alfanu ba a siyasantar da shi ba.

Shugaban Jam’iyyar APC ta Jihar, Alhaji Isah Sadik Achida ya bayyana haka a takaradar da ya sanaya wa hannu aka raba wa manema labarai a Sakkwato, inda ya ce APC ta ji abin da gwamnatin PDP ta fada cewa ta kashe Naira biliyan 19 a ginawa da gyaran ajujuwa cikin shekara biyar. “Ta yaya za mu tabbatar da gaskiya, jiharmu na bukatar hakan. Kaso da yawa na dalibai suna zaune kan dabe ne suna karbar darasi don ba kujerin zama a cikin ajujuwa. Malamai a Sakkwato an bar su baya a wurin karbar albashi, a duk wata sai sun shiga cikin mako na biyu kafin su amshi albashinsu,” inji Achida.                                                                                                                                                 A ranar Lahadi ce Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce ta kashe Naira biliyan 19 a bangaren ilimi wajen ginawa da gyara ajujuwan karatu 948 a sassan jihar tun daga 2015 zuwa yanzu, inda ta ce, ta gina sababbin ajujuwan karatu 388, ta gyara 460.

Gwamnan Jihar, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da kason gwamnati tare da bayar da kwangiloli ga mutum 200 da suka samu nasarar samun aikin, a taron da aka gudanar a harabar Hukumar Ilimin Bai-daya ta jihar da ke Sakkwato.

Gwamnan ya ce kudin da aka kashe suna cikin kudin tallafi na Gwamnatin Tarayya da Hukumar Ilimin Bai-Daya ta Kasa da yawansu ya kai Naira biliyan 7.2 da wasu kudin tallafi da aka samar ta Ma’aikatar Kananan Hukumomi da yawansu ya kai Naira biliyan 6.

Gwamnan ya ce kudin da gwamnatin ta kashe sun hada da Naira biliyan 2 a shirin Dorewar Muradun Karni (SDGs) inda aka gina ajujuwan karatu ba tare da jiran tallafin Gwamnatin Tarayya ba.

Gwamna Tambuwal ya kara da cewa gwamnatinsa ta fahimci akwai dimbin dalibai da ke bukatar ilimin firamare kan haka suka ware kashi 26 na kasafin kudinsu don gina  ajujuwan karatu.