✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kashi 30 na daliban Jami’ar Musulunci ta Uganda ba Musulmi ba ne’

Shugaban Jami’ar Musulunci da ke Uganda (IUIU), Dokta Ahmad Kawesa Segendo , ya ce kashi 30 cikin 100 na daliban jami’ar 8,500 ba Musulmi ba…

Shugaban Jami’ar Musulunci da ke Uganda (IUIU), Dokta Ahmad Kawesa Segendo , ya ce kashi 30 cikin 100 na daliban jami’ar 8,500 ba Musulmi ba ne.

kungiyar Hadin Kan Musulmi (OIC) ce ta kafa jami’ar domin cike gibin fannin ilimi a tsakanin Musulmi, kuma jami’ar ta fara aiki ne a 1988.

Shugaban wanda yake magana a lokacin da ya ziyarci Hedkkwatar Kamfanin Media Trust, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya a shekaranjiya Laraba, ya ce duk da cewa koya kyawawan dabi’un Musulunci ne babbar manufar jami’ar, amma ba ta takaita daukar dalibanta ga Musulmi kadai ba.

“An dora mana alhakin yin hidima ga kasashen Afirka masu amfani da harshen Ingilishi.. Falasafarmu a matsayin cibiya, ita ce ingantaccen ilimi da kyawawan dabi’u. Kuma game da haka muna fatan mu gina wani rukunin matasa maza da mata wadanda ba ilimi kawai za su samu ba, har ma da kyawawan dabi’u,” inji shi.

Ya ce, matsalar Afirka ba ta karancin wadanda suka kammala jami’a ba ne, a’a yankin ya rasa daidaikun mutane masu kyawawan dabi’u da rikon amana da kuma tarbiyyar rashin satar dukiyar gwamnati.

Kawesa ya ce sama da ’yan Najeriya 300 ne suke karatu a jami’ar a yanzu, yayin da fiye da dubu daya suka kammala ta.

Dokta Ahmad ya ce jami’arsa na koyar da fannonin kimiyyar halayyar dan Adam da harkokin shari’a da Larabci da sauran fannonin ilimin kimiyya. Kuma akwai bukatar ’yan Najeriya su dauka cewa jami’ar tasu ce.

Shugaban wanda ya samu rakiyar jakadun jami’ar da suka hada da Dokta Alhaji Abba Inuwa da Alhaji Abubakar Muhammad Ndagi da wadansu ’yan Najeriya biyu da suka hada da tsohon shugaban daliban makarantar na Afirka ta Yamma, ya bukaci kulla alaka da Kamfanin Media Trust don daliban da suka kammala jami’ar suka rika zuwa koyon aiki.

daliban da suka zama jakadun jami’ar a Najeriya sun bayyana gamsuwarsu kan irin tarbiyyar da jami’ar take bayarwa. Kuma sun ce akwai arahar rayuwa a kasar Uganda, ta yadda a cewar Dokta Abba Inuwa, Naira dubu 20 za ta iya daukar dawainiyar dalibi na tsawon wata uku.