✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashi 75 na ’yan Najeriyya sun gaji da mulkin PDP –Yahaya Sa’adu

kungiyar Hada Kan Mutanen Arewa ta shiga cikin masu zawarcin tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau don ya tsaya takarar Shugaban kasa a zaben…

kungiyar Hada Kan Mutanen Arewa ta shiga cikin masu zawarcin tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau don ya tsaya takarar Shugaban kasa a zaben shekarar 2015.  A tattaunawa da Mataimakin Shugabanta na kasa, Alhaji Yahaya Sa’adu ya bayyana dalilansu na wannan yunkuri, kuma ya ce halin da Jam’iyyar PDP ta samu kanta amsa addu’ar talakawa ne Allah Ya yi:

Aminiya: Mene ne dangantakar wannan kungiya da Malam Ibrahim Shekarau?
Yahaya Sa’adu: Malam Ibrahim Shekarau bai san da wannan kungiya ba, kuma bai da wata alaka da ita. Jama’ar da suka kafa kungiyar ce suka san shi ta tsarin ayyukansa da taimakonsa ga al’umma da kasa kan yadda komai zai zamo mai alheri a kasa baki daya.
Aminiya:  Me ya sanya kuke ganin Malam Shekarau ya cancani tsayawa takarar Shugaban kasa, a zaben shekarar 2015?
Yahaya Sa’adu: Dalilanmu kan bukatar Malam Ibrahim Shekarau ya tsaya takarar Shugaban kasa a zaben shekarar 2015 shi ne saboda
irin kokarin da ya yi a lokacin da ya yi shekara 8 a kujerar Gwamnan Jihar Kano.
Mun ga irin ayyukan raya kasa da ya yi a lokacin da irin taimakon da ya yi wa al’ummar jiharsa. Don haka muka ga ya kamata ya zo ya tsaya takarar Shugaban kasa, domin ya kawo canji kan mawuyacin halin da muke ciki a kasar nan.
Aminiya: Zuwa yanzu wadanne irin shirye-shiye kuka yi don cimma nasara kan wannan buri naku?
Yahaya Sa’adu: To babban abin da muka sanya a gaba shi ne Malam Ibrahim Shekarau ya amsa wannan kira da muke yi masa, kuma muna fatar zai amsa. Idan ya amsa muna rokon Allah ya kai shi ga kujerar shugabancin kasar nan.
Al’ummar Arewa da kasar nan za su samu wadatuwar alheri da zaman lafiya, idan Shekarau ya mulki kasar nan.
Aminiya: Ganin halin da kasar ke ciki, kuna ganin Malam Shekarau zai iya shugabancinta?
Yahaya Sa’adu: kwarai da gaske, dalilin da ya sanya ma muke son mu jawo shi ke nan. Saboda muna yi masa kyakkyawan zato cewa zai fitar da kasar nan daga yanayin da take ciki, lura da salonsa na iya mulki. Shekaru mutum ne da ya san harkar mulki, musamman idan muka dubi irin abubuwan da ya yi kafin ya zama Gwamnan Jihar Kano da abubuwan da ya yi a
lokacin da yake Gwamnan.
Haka kuma ya ba da gagarumar gudunmawa wajen ganin an samu nasarar kafa Jam’iyyar APC.
Aminiya: Ba ku ganin akwai wadanda suka fi shi cancantar takarar shugabancin kasar nan a Jam’iyyar APC?
Yahaya Sa’adu: Har yanzu ba mu ga wanda ya fi shi cancanta ba. Kuma wannan tsari ne na dimokuradiyya kowa ya fito ya tsaya a zabi wanda yafi cancanta.
Aminiya: Kuna ganin Jam’iyyar APC za ta iya ba Malam Shekarau wannan dama?
Yahaya Sa’adu: Lallai muna fatar haka za ta samu, kuma muna sa ran haka.
Aminiya: Me za ka ce kan dambarwar da ke faruwa a Jam’iyyar PDP a yanzu?
Yahaya Sa’adu: Dama talakawan Najeriya sun dade suna addu’ar Allah Ya kawo masu irin wannan lokaci da Jam’iyyar PDP za ta shiga cikin rikici. Kuma ga shi Allah Ya amshi addu’arsu. A cikin kashi 100 na mutanen Najeriya, kashi 75 sun gaji da mulkin Jam’iyyar PDP. Don haka suke ta addu’a Allah Ya kawo musu canji kuma ga shi Allah Ya kawo musu canjin. Don haka da ikon Allah PDP za ta zama sai labari a zaben shekarar 2015.
Aminiya: Wane sako ko kira ne kake da shi ga al’ummar Najeriya?
Yahaya Sa’adu: Sakona ga al’ummar Najeriya, shi ne mu yi hakuri da juna mu hada kai cikin alheri mu yi abin da zai zamar wa kasa
alheri. Kuma muna neman goyon bayan ’yan Najeriya, kan ba Malam Ibrahim Shekarau dama ya tsaya takarar Shugaban kasa, kuma sum zabe shi ya jagoranci kasar nan a zabe mai zuwa.