✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar Dabbobi ta Anagada Abuja za ta kunshi masu kayan abinci

Jagororin sabuwar Kasuwar Dabbobi ta Abuja da ke kauyen Anagada kusa da mahadar Giri Abuja, sun bayyana aniyar rungumar sauran ’yan kasuwa da ke harkar…

Jagororin sabuwar Kasuwar Dabbobi ta Abuja da ke kauyen Anagada kusa da mahadar Giri Abuja, sun bayyana aniyar rungumar sauran ’yan kasuwa da ke harkar kayan abinci don bunkasa hada-hadarta da kuma samar wa mazauna Birnin Tarayya kayan abinci cikin sauki. Babban Daraktan Kasuwar wadda ta hadin gwiwa ce da sojoji da suka samar da filin gudanar da ita, Alhaji Ayuba Umar Rano ne ya bayyana haka a yayin zantawa da Aminiya.

Ya ce kasuwar wadda Babban Hafsan Sojin Kasa Laftana Janar Tukur Yusuf Burtai ya kaddamar a watan Junairun bana, tana samun bunkasa cikin hanzari inda fataken dabbobi da Fulani makiyaya da mahauta ke haduwa a wajen bayan kowane rana 4 don gudanar da harkokin kasuwanci, baya ga bangaren dabbobin turke da ake sayar da su a kasuwar kullum.

Ya ce kasuwar ta fitar da filin rumfuna da za su kai dubu 5 don masu sayar da kayan abinci da suka hada da hatsi da doya da kayan lambu da  sauransu don gudanar da harkokinsu cikin tsanaki musamman lokacin damina ko zafin rana.

Sarkin Fawan Kasuwar Alhaji Sallau Jibrin Kibiya wanda ya zagaya da wakilinmu sashin mahautar zamani da ake ginawa yanzu haka, ya ce za ta kunshi na’urorin zamani don aiwatar da aikin nama ga abokan huldarta tare da kai naman zuwa inda ake bukata, baya ga shirin sarrafa nama zuwa nau’o’i daban-daban don safararsa zuwa kasashen waje.

Babban Sakataren Kamfanin Collectibe Bentures Nigeria Limited wanda shi ne ke raba fili a kasuwar, Barista Saleh Magama ya ce akwai shirin gina shaguna dubu 10 a kasuwar nan gaba baya ga samar da wajen yada zango ga manyan motocin kaya, saboda wajen yana da girman hekta 60. Mataimakin Sakataren Kasuwar Malam Sa’idu Ibrahim ya ce yanzu haka kasuwar ta samar da dimbin sana’a ga matasan yankin baya ga iyaye mata da ke yin abincin sayarwa. Kuma akwai sojoji da suka yada zango a wani bangare na kasuwar don tabbatar da an samu cikakken tsaro.