✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar takunkumi ta yi kasa a Kano

Yayin da aka shiga mako na biyu da cirea dokar kulle a jihar Kano, Aminiya ta lura cewa yanzu cinikin da dama daga kayan da…

Almajirai 193 sun kamu da coronavirus a Kano
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Yayin da aka shiga mako na biyu da cirea dokar kulle a jihar Kano, Aminiya ta lura cewa yanzu cinikin da dama daga kayan da aka rika amfani da su lokacin dokar COVID-19 ta ya ragu matuka.

Takunkumi da sinadarin wanke hannu da sauransu sun ci kasuwarsu a lokacin dokar, amma yanzu ba a cinikinsu sosai, saboda akasarin mutane sun fara komawa rayuwarsu yadda suka saba.

“A baya nakan iya sayar da fakiti biyu na kyallen rufe fuska a kan titi, amma yanzu cinikin ya yi kasa matuka”, inji wani yaro da Aminiya ta iske yana sayar da kyallen a kusa da katafaren rukunin kantunan kasuwar zamani ta Ado Bayero Mall (Shoprite).

An daina sa takunkumi ne?

Aminiya ta lura cewa ba kasafai mutane ke sanya kyallen a fuskarsu ba, duk kuwa da cewa gwamnati ta sanya dokar yin hakan.

Wani fasinja da ke kan babur mai kafa uku da aka fi sani da A daidaita Sahu, Jamilu Garba, ya ce yawancin mutane ba sa amfani da shi ne saboda jami’an tsaro ba sa tursasa musu yin hakan.

“Tsakani da Allah in ka ga na rufe fuska ta da kyalle to kodai wurin da zan shiga sun tilasta sakawa a matsayin sharadin shiga, ko kuma idan ban saka ba jami’in tsaro zai kama ni ko ya ci ni tara.

“Amma in dai ba dayan wadannan dalilan ba, ban ga dalilin da zai sa in ta yawo da takunkumi a fuskata sai kace kura ba.

“Maganar da nake maka yanzu haka ina da kyallen a aljihuna, amma nakan saka shi ne kawai a inda bukatar hakan ta taso”, inji Jamilu.

Yawancin mutane a Kano dai na da ra’ayi makamancin na Jamil musamman la’akari da cewa ana kara samun raguwar sabbin kamuwa da cutar a ‘yan makonnin nan.

Tazara ba za ta yiwu ba

A bangaren masu tuka baburan A daidaita Sahu kuwa, direbobi sun ci gaba da daukar fasinjojinsu kamar yadda suka saba a baya, sabanin dokar da gwamnatin jihar na daukar mutane biyu kacal.

Kan batun wannan dokar dai, direbobin sun ce ba za ta sabu ba.

Nura Goga, wani direba ya ce, “Yanzu fisabilillahi ta yaya za ka ce mutum biyu zan dauka. Ta yaya zan iya hada kudaden da zan kai wa mai babur din a haka? Ga kuma harajin da gwamnati take karba a hannunmu hawa-hawa.

“Idan ma ance zaman mutum uku zai iya kawo cutar corona, to wadanda ke cudanya a kasuwa da gidajen kallo su kuma meye makomarsu?”, in ji Goga.

Ya zuwa daren Laraba dai, jihar Kano ita ce jiha ta shida da ta fi yawan masu dauke da cutar COVID-19 da mutum 1,291 da wuka kamu.

1,029 sun warke kuma tuni an sallame su, yayin da mutane 52 kuma suka riga mu gidan gaskiya.