✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar ‘yan kwallo: Chelsea za ta dauki Mertens, kungiyoyi da dama na son Cavani

Kungiyar Everton ta ki karbar tayin Yuro miliyan 100 daga Barcelona kan dan wasan gabanta dan kasar Brazil mai suna Richarlison, kamar yadda aka sanar…

Kungiyar Everton ta ki karbar tayin Yuro miliyan 100 daga Barcelona kan dan wasan gabanta dan kasar Brazil mai suna Richarlison, kamar yadda aka sanar a rahoton Sky Sports

Shafin Livrpool Echo ya rawaito cewa Everton din ta nanata cewa Richarlison mai shekara 22 ba na sayarwa ba ne kuma tana shirin gina kungiyar a kansa.

Barcelona na neman dan wasan gaba ruwa a jallo kafin rufe kasuwar saye da musayar ‘yan kwallo a makon nan sakamakon raunin da Luis Suarez yake fama da shi. Sport ta rawaito.

Tottenham ta tattauna da Real Madrid kan Gareth Bale mai shekara 30, in  ji jaridar Mail.

Chelsea ta fara tattaunawa da kungiyar Napoli domin daukar Dries Mertens mai shekara 32, wanda zai kai fan miliyan 6, a rahoton Mail.

Sai dai jaridar Guardian ta rawito cewa Mertens, wanda kwantaraginsa zai kare a karshen kakar bana, ka iya maye gurbin Edinson Cavani a kungiyar PSG.

Har wa yau, Telegraph ta rawaito cewa Napoli ba ta son sayar da dan wasn yayin da aka kusa rufe kasuwar, inda ita kuma Chelsea take kara matsa kaimin daukarsa.

Atletico Madrid ta ki ta bai wa PSG sama da yuro milyan 15 kan Edinson Cavani. (Le Parisien – in French)

Kazalika kungiyar Inter Miami ta Amurka mallakar David Beckam tana sha’awar daukar Cavani, in ji AS.

Tottenham na tattaunawa don daukar Willian Jose mai shekara 28 daga Real Sociedad. (ESPN)