✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwar ‘yan wasan Turai: Bale zai iya komawa Tottenam, Chelsea na son Cavani

Real Madrid ta shirya tsaf domin tattauna komawar Gareth Bale mai shekara 30 zuwa Tottenham amma tana fargabar kulla kowace irin yarjejeniya, a cewar rahoton…

Real Madrid ta shirya tsaf domin tattauna komawar Gareth Bale mai shekara 30 zuwa Tottenham amma tana fargabar kulla kowace irin yarjejeniya, a cewar rahoton jaridar Telegraph.

Mahaifin dan wasan gaban kungiyar PSG, Edinson Cavani mai shekara 32, y ace dan was an zai koma Atletico Madrid idan kulob din na kasar Spain ya iya kulla wata yarjejeniya, in ji rahoton jaridar Guardian.

Edinson Cavani

Kungiyar Chelsea kuwa ta nuna sha’awar daukar Cavani din a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana, jaridar Times ta ruwaito.

PSG na bukatar akalla yuro miliyan biyar daga Arsenal kan dan wasan bayanta da take son dauka mai suna Layvin Kurzawa  wannan watan, a cewar jaridar Telegraph.

Tottenham ta nemi dan wasan kungiyar Real Sociedad uma dan kasar Brazil mai suna Willian Jose kuma dan was an ai shekara 28 zai je birnin Landan domin tattaunawa, jaridar AS ta ruwaito.

Leicester City ta kusa cimma yarjejeniyar daukar dan wasan baya Jannik Vestergaard mai kuma dan kasar Denmark mai shekara 27 daga Southampton kan fan miliyan 15, in ji jaridar Sun.

Bayern Munich ba za ta yarda ta ki sayen Philippe Coutinho, wanda yake buga mata wasa aro a yanzu daga Barcelona, a cewar jaridar Mirror.

Kungiyoyin Premier shida ne suke son daukar dan wasan bayan Tottenham n bangaren hagu, Danny Rose mai shekara 29 a wannan watan na Janairu, in ji Sky Sports.