✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kata-katar kutungwilar kandame kunu

Kata-katar karbar kwanon kunu Kunkurun kururuwar kurkunu Kanwa katuwar ungurnu Kurbar shan ruwan shanu Karime-karimen maganganu   Zabarin zagon kasan zabge zabe Zazzzagar zuga-zugi ta…

Kata-katar karbar kwanon kunu

Kunkurun kururuwar kurkunu

Kanwa katuwar ungurnu

Kurbar shan ruwan shanu

Karime-karimen maganganu

 

Zabarin zagon kasan zabge zabe

Zazzzagar zuga-zugi ta babe

Kutungwila ta kwabe

Kandamar kunu za ai a kurbe

Baba sabi zarce rigarka ce a sabe

 

Hukumar zabi-sonka

Ta baro da masu toliyar ka

Sun yi kulla-kullar kiki-kaka

Haddar sarkakiyar karatun sauka

Kulun kolon garada yai kuka

 

Dabarbarun dangwale

Daddalewar dole

Dalilin dauje dudduge

Duddugar dage-dage

Dambarwar dangale

 

Makon da ya arce

An yi ka-ce-na-ce

Makirai sun so yin kwace

Kuri’unmu aka so a wafce

Danboto rumfar kwace

 

Lamarin sai da kwatance

Amma ba habaice-habaice

Na ji ana ta yawan zance

A jaridu mun yi karance-karance

Tsaba da tsakuwa an tantance

 

Kai tsohuwa ta iya rummace

Rama da garin gero an yi kawance

Kwado ne a mutunce

An fasko nufin Turance-Turance

Mulkin mulaka’un bambance-bambance

 

Barazanar Batoyi

Burgar janye majanyi

Goyon jariri za a daina yayi

Kuturin ingarman darewar mahayi

Dimbin darussan koyi

Miyagu sun so jefa layin laulayi

 

Nawa dai shi ne labari

Shugaba muke so nagari

Makarin kofa gambu da asabari

Ba rafkiyar wakilan garari

Dundumin duhun Dogari dagirgiri

 

Samarin-kusu nake hantari

Kar su jefa kasa hadari

Haduwar hadari

Sama ta tsuge da bari

Haurobiyawa a kara kokari

 

Asibicin da ta rare a guje, Haurobiyawa sun sha jaje bayan da aka kama masu nadin lauje suna ta kidan jauje a KATA-KATAR KUTUNGWILAR KAMDAME KUNU, wai da zimmar dandanawa su ji wai NA TSAMIYA ne ko na UNGURNU, sai muguwar manufarsu ta yi wuntsila gudi-gudi tamfar an sa musu HANNU. An dai yi Zabarin zagon kasan zabge zabe, ta hanyar DABAREWAR DABEN DABAI, inda aka yi ta kulla kutungwila iri-iri, tare da salon sole fatar jiki da sabulun salo.

Haurobiyawa, Shugaban Hukumar Zabi-sonka na kasar nan ya baje batutuwa ta kafar kwaratsin kalallame kalamai mai baje wutsil-wutsil din dodannin hotuna, inda ya dora wa kurungunsa alhakin duk wata bahallatsa da aka tsiwurwurta, wadda ta kai ga kawo tsaikon tsayar da zababbakar zabuka cik, har zuwa Asibicin makon nan, inda za a fafata fafutikar FAFE-BAURE, ba tare da bare-bare ba, uwa-uba hukumar ta ja na-zomon masu fuka-fukin tashi lallai duk wanda aka damke yana sare-sare, ko sare-sarin satar sundukin saka kuri’u, to za a gasa masa aya a kurungu.

Lallai mu daina baza jita-jitar jikkata jakkan dakon danboto da sanda jirge, wadda aka tabbatar ita ce babbar rumfar wa-ka-ci-ka-tashin wafce-wafce da sace-sace, tunda su suka jefa kasar nan cikin DUHUN-DUNDUM-DURUN-DUM. Hujja kuwa a kan wannan batu ita ce salwantar da Damin DALAR AMURKAWA sili da manuniyar sama da aka tsiwurwurta a zamanin jan ragamar Baba-Ojo mai gonakin Ottawa. Dadin dadawa Dagirgirin Dogarin wakilan rafkanuwar rafke al’ummar kasar nan ya tabbatar da cewa an yi salular salalar sulallan kasar nan har Hauro tiren taliya karamin lauje da gashin balama dari kwanciyar magirbi wajen cefano wa kasar nan DUHUN-DUNDUM-DURUN-DUM, a zamanin mulkin mulaka’u na jam’iyyar mai dan boto da sanda jirge. Watakila so suke su sake samun damar DAMA-DAMAR DAMALMALA al’amura, har su jefa kasar nan a matsanancin duhu, don su ci gaba da KURUCIYAR BERA, yadda SAMARIN-KUSU da ’YAN MATAN JABA DA GAFIYA za su ji dadin watayawa.

’Yan makaranta masu koyon watsattsake da falle shafukan mujallu da makalu da wagagen littattafai, mu zaburar da Baban-burin-huriyya da mataimakinsa Usainin-Babajo kan lallai su ci gaba da jan zugar masu share mana jibgin jibar da aka jibga mana, musamman kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma. Kada mu bayar da kafa Baba-ojo da kannensa su zo su sake mayar da hannayen wulwulawar agogo baya.

Kai hatta BALBALIN BALA’IN BANKE BOBO DA KWAMBON BOKOKO, an ta’allaka shi da ta’asar da aka tafka zamanin Jan ragamar GUDUN-LOKO da JONA-TANTIN MULKI, a karkashin tutar jam’iyyar mai danboto da sanda jirge. Kai su SAMUN-BOM-DA-SAUKI su ci kolonsu babu babbaka.

Batu na ingarman karfafan karafan karfa-karfan titin tarragon layin dogo, babu bata lokacin wulkitawar tsinkayen manuniyar yanayin loto-loto, ya zama wajibi ga daukacin al’ummar Haurobiya su yi watsi da batun RUMFAR BERAYE, wadanda suka kudiri aniyar tsiwurwurta WATANGARIRIYAR WA-KA-CI-KA-TASHIN WAWAR WAWAYE. Jiki dai magayi BANKAR BUKIN DAN KORAU!

Burin kowane mai hankali da halin samun halali, shi ne kasar nan ta kasance karkashin rikon jagorancin shugabanni nagargaru, bisa wannan dalili ne,sai mu baje na-mujiyarmu kuru-kuru, domin mu moru ka da mu kwaru!