katar: Sarkin da ya kwace mulki daga mahaifinsa, ya mika wa dansa

Sarkin katar, Sheikh Hamad bin Khalifa al-Thani, wanda yakwa ce mulki daga hannun mahaifinsa, bayan ya shafe shekara 18 yana ghudanar da harkokin mulki, ya sauka ya mika wa dansa ragamar, mai suna Sheikh Tamim, dan sheakra 33.
“A yau ina mai sanar da ku cewa na mika mulki ga Sheikh Tamin bin Hamad al-Thani,” a cewar sarki mai murabus, dan shekara 61, a jawabin da ya yi wa al’ummar kasar katar, aka kuma watsa ta tashar talabijin.
Wannan mataki da sarkin ya dauka, an danganta shi da matsalar rashin lafiya, musamman bisa  la’akari da cewa ya yi fama da ciwon koda. Sai dai jami’an hukuma sun bayyana cewa, wannan murabus da sarkin ya yi ba shi da wata nasaba da rashin lafiya, ya yi ne a kashin kansa, don ya bayar da dama ga matasa  su gabatar da jagorancin kasar.

Share