✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katrina, Ranbir sun rakashe a Sri Lanka

A makon da ya gabata ne jaridar ‘India Times’ ta ruwaito cewa soyayyar da ke tsakanin jaruman fim, Ranbir Kapoor da Katrina Kaif tana kara…

Masoya biyu a Sri Lanka, Ranbir Kapoor da Katrina KaifA makon da ya gabata ne jaridar ‘India Times’ ta ruwaito cewa soyayyar da ke tsakanin jaruman fim, Ranbir Kapoor da Katrina Kaif tana kara ruruwa, musamman ma da aka samo labarin yadda suka rakashe a kasar Sri Lanka.
A makon na jiya ne al’ummar Indiya suka wayi gari da hotunan masoyan biyu, yayin da suke yawon shakatawa a kasar Sri Lanka. Hotunan da masoyan suka yi bakin cikin bayyanarsu, musamman saboda kasancewar sun bayyana wasu daga cikin tsiraicinsu. Domin nuna rashin gamsuwarsu da yadda aka yada hotunan, Katrina Kaif ta rubuta wasikar koke, ta rarraba wa gidajen jaridu.
Wani dalili da ya kara tabbatar da cewa soyayyar tasu ta gawurta shi ne, yadda duk da cewa Ranbir da budurwar tasa sun je kasar Sri Lanka ne da nufin aikin fim din Furodusa Anurag Kashyap, mai taken ‘Bobay belbet in Sri Lanka’ amma suka rika samun lokaci suna rakashewa.
A yayin da suke wannan jerangiyar soyayya ne, su kuma ’yan jaridar hoto suka samu aikin yi, suka rika yadawa da tallata hotunan nasu, wanda hakan bai yi masu dadi ba.